Harin Isra'ila a kan Al-Nujaba Shelar Yaki ne: Asa'ib Ahl al-Haq


Shugaban kungiyar Asa’ib Ahl al-Haq na kasar Iraki Qais al-Khazali ya ce harin baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kan kungiyar gwagwarmaya ta Al-Nujaba ta Iraki ba wani sabon abu ba ne, kuma a halin yanzu Kungiyar na cikin yanayin yaki.


Al-Khazali ya bayyana hakan ne a ranar Asabar kwanaki biyu bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta harba makamai masu linzami daga tuddan Golan da ta mamaye zuwa wajen Damascus babban birnin kasar da suka auka kan ofishin yada labarai na Al-Nujaba.


Ma'aikatar tsaron Siriya ta tabbatar da harin wanda ta ce an kai harin ne a wani gini a yankin Damascus. Ma'aikatar ta kuma ce dakarun tsaro sun harbo makamai masu linzami na Isra'ila.


Gwamnatin 'yan mamayar ta gudanar da harin ne a daidai lokacin da kungiyar Al-Nujaba ke kai hare-hare kan Isra'ila a matsayin mayar da martani ga yakin da gwamnatin 'yan mamayar ke yi a Gaza inda kusan Falasdinawa 35,000 suka rasa rayukansu tun farkon watan Oktoba.


Al-Khazali ya shaidawa gidan talabijin din Al-Ahed ta kasar Iraki cewa harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai ba sabon abu ba ne kuma kungiyoyin gwagwarmaya na Iraki na cikin yanayin yaki.


Ya kuma ce gwamnatin Irakin za ta ci gaba da goyon bayan al'ummar Palastinu, amma ba ta bukatar daukar matakin soji saboda rawar da kungiyoyin 'yan gwagwarmayar kasar ke takawa a madadin gwamnati.


Tun da farko dai kungiyar Al-Nujaba ta tabbatar da harin da aka kai kan ofishin yada labaranta a kasar Siriya tare da yin alkawarin daukar fansa ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka a cikin yankunan da aka mamaye."


Allah ya taimaki 'yan gwagwarmayar Musulunci a duk inda suke ya kuma basu Nasara.

Post a Comment

Previous Post Next Post