An harba makamai masu linzami 55 da rokoki daga Lebanon zuwa Arewacin Falasdinu da HKI ta mamaye


Kafofin yada labaran Isra'ila sun bayar da rahoton cewa, an harba makamai masu linzami 55 da rokoki daga kudancin Lebanon zuwa Palasdinu da ta mamaye a arewacin kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Mayadin cewa, kafofin yada labaran gwamnatin yahudawan sahyoniya sun sanar da cewa, sakamakon wadannan makamai masu linzami da aka harba a matsugunin "Kariat Shmoune", an yi barna mai yawa ga gidaje da ababen more rayuwa na wannan matsugunan.


Kafofin yada labaran yahudawan sahyuniya sun kuma bayar da labarin kokarin da ma'aikatan kashe gobara suka yi na kashe gobarar data faru sanadiyyar wadannan makamai masu linzami daka aka harba a Kiryat Shmoune.


Kungiyar gwagwarmayar muslunci ta kasar Labanon ta sanar a cikin wata sanarwa cewa, a matsayin mayar da martani ga hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da kai wa a garuruwa da kauyukan kasar Labanon da kuma kai wa fararen hula hari, ta kai hari kan Kiryat Shmouneh da kuma Katyushas.

Post a Comment

Previous Post Next Post