'Yan Gwagwarmayar Islama dake Iraqi Sun kai Sabbin Hare-hare a Wuraren da Isra'ila ta Mamaye


Kungiyar Gwagwarmayar Islama dake Iraki ta ce ta kai wani sabon hari a yankunan Falasdinawa da HKI ta mamaye.

Kungiyar Gwagwarmayar Islama dake Iraqi, wato kungiyar nan ta mayaƙa wanda suke yaƙi da ta'addanci, a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na Telegram, ta dauki alhakin harin da aka kai a muhimmin guri a tashar jiragen ruwa ta "Eilat" a yammacin Juma'a.

Kungiyar ta ce harin da suka kai da jirgi mara matuki sun kai shine a matsayin mayar da martani ga kisan kiyashin da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ke yiwa fararen hulan Falasdinawa.

Kungiyar ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare kan matsugun nan Isra'ila.

Kungiyar Gwagwarmayar ta Islama takai ire-iren waɗannan hare-hare masu yawa kan wuraren 'yan mamayar, tun lokacin da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta kaddamar da yaƙin kisan kare dangi a Gaza a farkon Oktoban shekarar da ta gabata.

Har ila yau, ta kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka dake Iraki da makwabciyarta Syria a matsayin ramuwar gayya ga goyon bayan da Washington ke ba wa Isra'ila akan kisan kare dangi da suke yi a Gaza.

Haramtacciyar Kasar ta Isra'ila ta kaddamar da wani mummunan hari a zirin Gaza, inda ta dinga kai hari kan asibitoci, gidaje da guraren ibada da sauran su.

Wannan farmakin ya fara ne bayan da kungiyar gwagwarmayar Falasɗinu suka kaddamar da wani farmakin ba-zata, wanda aka fi sani da Guguwar Al-aqsa, kan 'yan mamayar a ranar 7 ga watan Oktoba, domin mayar da martani kan abinda HKI keyi akan al'ummar Falasɗinu.

Wanda hakan ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 35,800, wadanda akasarinsu mata da yara ne, ya kuma yi sanadiyyar jikkata wasu 80,200. Bugu da kari, sama da mutane miliyan 1.7 ne suka rasa matsugunansu sakamakon yakin.

Post a Comment

Previous Post Next Post