No title


Dakarun Ansarullah na Yemen sun sanar da kaddamar da hare-hare guda uku masu goyon bayan Falasdinawa, inda suka kai hari kan jiragen Ruwan Isra'ila guda biyu dayan kuma ya nufi yankunan da aka mamaye.

Kakakin rundunar Birgediya Janar Yahya Saree ne ya bayyana hakan a babban birnin kasar Sanaa a ranar Juma'a.  Ya yi jawabi ne a wani taron dubban mutane da aka gudanar domin nuna goyon baya ga Falasdinawa dake zirin Gaza, wadanda ke fama da yakin Isra'ila na kisan kare dangi.

 "Harin farko ya nufi jirgin Isra'ila MSC Alexandra a cikin tekun Larabawa da makamai masu linzami da dama," in ji shi.

Jami'in ya ce, "Hari na biyu kuma sojojin ruwa, sojojin sama, da kuma sojojin makami mai linzami ne suka kaishi, inda suka hari Jirgin ruwan Yannis yayin da yake ratsa tekun Bahar Maliya" zuwa yankunan da aka mamaye.

Saree ya ce, "Rundunar makami mai linzami (Missile Force) ne suka kai hari na uku, inda suka hari jirgin ruwan 'Isra'ila' Essex a cikin tekun Bahar Rum."

Kasar Yemen ta fara kai hare-hare ne bayan 7 ga watan Oktoba, lokacin da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta kaddamar da yaƙi a Gaza wanda ya zuwa yanzu ya kashe Falasdinawa akalla 35,800, galibi mata da kananan yara, tare da jikkata wasu 80,200.

Sojojin Yaman sun fara kai harin ne ta hanyar kai hari kan jiragen ruwa na Haramtacciyar Kasar Isra'ila ko kuma wadanda ke kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa na yankunan Falasdinawa da suka mamaye da za su iya wucewa ta yankunan ruwa na Yemen.

A hankali sun fadada hare-haren su don rufe duk yankunan da aka mamaye, da kuma jiragen ruwa da ke tafiya akan tekun Indiya, yayin da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta ki amincewa da bukatarsu ta dakatar da kisan kiyashi da kuma kawanya da take yi a lokaci guda a Gaza.

A farkon watan Mayu, Saree ya ba da sanarwar fara kashi na hudu na hare haren goyon bayan Falasdinawa, yana mai cewa sojojin Yemen za su kai hari kan dukkan jiragen ruwa da ke kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa na "Isra'ila" a cikin tekun Bahar Rum a kowane yanki da za mu iya isa.

Da yake karin haske game da jawabin nasa, kakakin ya ce, "Rundunar sojan Yaman ta sake sabunta gargadin da suke yi ga duk kamfanonin da ke hulda da Haramtacciyar Kasar Isra'ila cewa jiragen ruwansu ba tare da la'akari da inda suke ba, za'a kai masu hari muddin suka shiga yankin da aka ayyana.

Post a Comment

Previous Post Next Post