Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta Musamman Mai Kawo Rahoto Kan Halin da ake ciki na kare hakkin bil adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese ta yi kira da a kakaba takunkumi kan gwamnatin Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila.
Albanese ta jaddada a jiya Asabar cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kara tsawaita kai hare hare a birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza biyo bayan hukuncin da kotun duniya ta yanke ranar Juma'a.
Mai kawo rahotan ta kuma ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ba za ta daina hauka da rashin hankali ba, sai dai idan kasashen duniya sun dakatar da ita, don haka dole ne a kakabawa gwamnatin takunkumi, da hana fitar da makamai zuwa gare ta, sannan a dakatar da huldar diplomasiyya da Tel Aviv har sai an dakatar da kai hari a Rafah.
Darektan sashen Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka na Amnesty International Heba Morayef ya kuma jaddada a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a daren Juma'a cewa duk wani matakin soji da zai kai ga kisan kare dangi dole ne a dakatar da shi; don haka dole ne jami'an Isra'ila su dakatar da ayyukan soji a Rafah gaba daya.
Morayef ya yi gargadin cewa, ko shakka babu kutsen da aka yi a ƙasa da kuma tilastawa mazauna Gaza kauracewa gidajensu ya haifar da babbar barazana da ba za a iya jurewa ba ga Falasdinawan da aka ba su hakkinsu a karkashin yarjejeniyar kisan kare dangi.
Mai shari'a Nawaf Salam na kasar Labanon, shugaban kotun kasa da kasa, ya ce bisa ga yarjejeniyar kisan kare dangi, duk wani hari da za'a yi a Rafah, zai iya haifar da rugujewar wani bangare ko kuma gaba daya wannan birni, don haka dole ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare a Rafah cikin gaggawa.
