
Babban jami’in harkokin wajen kungiyar EU Josep Borrell ya bukaci Haramtacciyar Gwamnatin Isra’ila da ta aiwatar da umarnin kotun duniya kan halin da ake ciki a Gaza, ciki har da umarnin dakatar da farmakin da sojoji ke kai wa a kudancin birnin Rafah.
Hukunce-hukuncen ICJ na karshe ne kuma dole ne a aiwatar da su gaba daya," in ji Borrell a dandalin sada zumunta na X ranar Asabar, kwana guda bayan da Kotun Duniya ta yanke hukunci kan karar da Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra'ila.
A cikin sakonsa na X, wanda a baya akafi sani da Twitter, babban jami'in diflomasiyyar EU yayi kira da abi umarnin ICJ ciki har da kira da a dakatar da kai hare-hare a Rafah cikin gaggawa, da kuma wani kira ga Isra'ila da ta bude mashigar birnin don ba da agaji.
Isra'ila ta kaddamar da farmaki a Rafah a ranar 7 ga watan Mayu, bayan da ta yi watsi da kiran da kasashen duniya suka yi na cewa kada taci gaba. Birnin ya Ɗauke da Falasdinawa kimanin miliyan 1.4 kafin gwamnatin ta fara kai hari, wanda a yanzu haka kusan Mutum 800,000 ne suka rasa matsugunansu, a cewar kotun ta ICJ.
Shari'ar Afirka ta Kudu ta neman dakatar da hare-haren Rafah wani bangare ne na karar da kasar ta shigar kan Isra'ila a babban kotun MDD a karshen watan Disamba kan kisan kiyashin da gwamnatin kasar ke yi a Gaza.
Kotun da ke Hague ta umarci gwamnatin kasar a watan Janairu da ta dakatar da kisan kiyashin da take yi a yankin Falasdinu.