Jama'a a gabar yammacin kogin Jordan da Lebanon sun yi ta kwarara kan tituna domin murnar kame sojojin Isra'ila a sansanin Jabalia da ke arewacin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Samaa na kasar Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, Jama'a a garuruwan Doura da Tyre na kasar Lebanon da kuma sansanonin 'yan gudun hijira na Falasdinawa na Ain Al-Hilweh, Nahr Al-Bared, Al-Bass da Al-Rashidiyah a kasar Lebanon sun fito kan tituna domin yin murna da kame sojojin yahudawan sahyoniya da dakarun Izz Al-Din al-Qassam, reshen soja na kungiyar gwagwarmayar Hamas suka yi.
Jama'ar yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye suma sun bazama kan tituna domin nuna farin cikinsu bayan masallaci, suka yi kira ga Falasdinawa da su yi murna a wannan lokacin.
Kakakin rundunar sojojin kasar ta Al-Qassam Brigades, Abu Ubaida, ya sanar da cewa, mayakan Al-Qassam sun kai wani gagarumin farmaki a arewacin zirin Gaza a yammacin Jiya Asabar, inda suka yi arangama da ‘yan kungiyar Isra’ila, inda suka kashe, suka jikkata da kuma suka kama wasu.
"Gwamnatin makiya tana tafiya daga Rashin nasara zuwa Rashin Nasara, kuma mujahidan mu suna ci gaba da koyar dasu darussa a fagen fama, kuma Sabuwar rashin nasara da suka yi itace abin da sojojin suka yi a Jabalia da Rafah," in ji Abu Ubaida.
Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta taya al'ummar kasar murnar wannan al'amari, inda ta ce dakarun Al-Qassam sun kawo abin alfahari ga al'ummar musulmi, tare da baiwa al'ummar musulmi mamaki, hakuri da juriya da nasarorin da suka samu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta kara da cewa farmakin na daya daga cikin hare-haren Jarumtaka da ya yi mummunar illa ga makiya yahudawan sahyoniya, kuma ya yi daidai da hakkin Falasdinawa na mayar da martani kan yakin kisan kare dangi a zirin Gaza.
