Dubban ‘yan kasar Afirka ta Kudu ne suka fantsama kan tituna domin nuna goyon bayansu ga Gaza da Falasdinu tare da rera taken nuna adawa da Isra’ila da yaƙin da ake yi.
Kafar yada labaran Falasdinu ta ce an gudanar da zanga-zangar ne a birnin Cape Town.
Har ila yau gwamnatin Afirka ta Kudu ta dauki matakai masu yawa na goyon bayan al'ummar Gaza da ake zalunta cikin 'yan watannin nan na yin Allah wadai da gwamnatin sahyoniyawan a sassan duniya, matakin da watakila kasashen musulmi da na larabawa da dama suka kasa yi.
A wani mataki na jajircewa, Afirka ta Kudu ta shigar da kara kan gwamnatin sahyoniyawan a kotun duniya ta ICJ.
Isra'ila ta kaddamar da farmaki a Rafah a ranar 7 ga watan Mayun da ya gabata, domin bijirewa kiraye-kirayen da kasashen duniya suka yi na kada su ci gaba. Birnin mai ɗauke da Falasdinawa kimanin miliyan 1.4 kafin gwamnatin ta fara kai hare hare, wanda a yanzu haka kusan dubu mutane 800,000 ne suka rasa matsugunansu, a cewar kotun ta ICJ.
Ƙarar Afirka ta Kudu ta neman dakatar da hare-haren Rafah wani bangare ne na karar da kasar ta shigar kan Isra'ila a babban kotun MDD a karshen watan Disamba kan kisan kiyashin da gwamnatin kasar ke yi a Gaza.
Kotun da ke Hague ta umarci gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila a watan Janairu da ta dakatar da kisan kiyashin da take yi a yankin Falasdinu.
