Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta sanar da cewa ba za ta shiga duk wata tattaunawa ba, bayan munanan laifuka da gwamnatin HKI ta aikata a sansanin 'yan gudun hijira da ke Rafah.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayar da rahoton cewa, kungiyar Hamas ta sanar a yau Litinin cewa ba za ta shiga wata tattaunawa ba sakamakon kazamin harin da sojojin yahudawan sahyoniya suka yi a sansanin 'yan gudun hijira a Rafah, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa da dama.
A baya dai a cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce gwamnatin Amurka da shugaban kasa Joe Biden ne ke da alhakin wannan aika-aika, domin da ba don goyon bayan Washington ba da gwamnatin yahudawan sahyoniya ba za ta iya aikata wannan laifi ba.
Hamas ta kuma bukaci da a gaggauta aiwatar da hukuncin kotun ICJ da kuma matsin lamba ga 'yan mamayar na su daina zubar da jinin fararen hula Falasdinawa da suka hada da mata da yara da kuma tsofaffi.
Har ila yau wannan yunkuri ya bukaci dukkanin bangarori musamman kasar Masar da su matsa lamba kan gwamnatin sahyoniyawan da ta janye dakarunta daga mashigar Rafah, domin ci gaba da gudanar da ayyukan wannan mashigar da kuma saukaka fitar da wadanda suka jikkata da marasa lafiya da isar kayayyakin agaji.
A sabon laifin da ta aikata kan Falasdinawa a tsakiyar daren jiya, gwamnatin sahyoniyawan ta kashe fararen hula 41 da suka hada da mata da kananan yara tare da jikkata wasu da dama a yankin arewa maso yammacin Rafah.
