Kasar Yemen ta kaddamar da sabbin hare-hare kan jiragen ruwa, da suka hada da Jirgin ruwan yaƙin Amurka a tekun Bahar


Kasar Yemen ta kaddamar da sabbin hare-hare kan jiragen ruwa, da suka hada da Jirgin ruwan yaƙin Amurka a tekun Bahar Maliya da kuma tekun Indiya, domin nuna Goyon Baya ga Al'ummar Falasdinu, da kuma tunkarar hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza. 

Jimillar jiragen ruwa guda biyar da suka hada da jiragen yakin Amurka guda biyu ne aka kaiwa hari a wani bangare na aiyukan sojin kasar Yemen a ranar litinin, a cewar kakakin rundunar sojin kasar ta Yemen Janar Yahya Saree. 


 Saree ya ce daga cikin jiragen ruwa guda biyu na Amurka da na Isra'ila da aka kaiwa hari a tekun Indiya sune LAREGO DESERT da MSC MECHELA. 


Wani jirgin ruwan Isra’ila mai suna MINERVA LISA ya fuskanci hare-haren da ‘yan kasar Yemen suka kai a tekun Bahar Maliya, ya kuma kara da cewa, an kai harin ne saboda jirgin ya saba wa dokar da kasar Yemen ta yi na hana jiragen ruwa zuwa tashar da Isra’ila ke iko da su.


"...Rundunar sojin sama ta kai wasu hare-hare guda biyu na musamman da aka auna wasu jiragen yakin Amurka guda biyu a cikin tekun Bahar Maliya, kuma anyi nasarar harin." in ji shi dangane da wasu hare-hare guda biyu da aka kai a ranar Litinin kan jiragen yakin Amurka. 


Tun a watan Nuwambar shekarar da ta gabata ne kasar Yemen ta fara kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da Isra'ila a wani bangare na yunkurin tallafawa mutanen Gaza kan hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke yi masu. 


 Hare-haren da kasar Yamen ke kaiwa ya fadada zuwa jiragen ruwan da ke da alaka da Amurka da Biritaniya a daidai lokacin da kasashen biyu ke kai hare-hare ta sama kan kasar Yamen don tilasta musu dakatar da ayyukan da suke yi na yaki da Isra'ila.


Muna Rokon Allah daya cigaba daba Wadannan bayi nasa nasara da kuma kariya dama sauran 'yan Gwagwarmayar Musulunci a duk inda suke, akan wadannan miyagu kuma shedanu.

Post a Comment

Previous Post Next Post