Wani harin makami mai linzami ya lalata wani jirgin ruwa a tekun Bahar Maliya da ke gabar tekun Yemen, kamar yadda wani kamfanin tsaro mai zaman kansa Ambrey suka sanar.
Jirgin ya lalace a harin da aka kai a yau Talata, kuma yanzu haka yana cike da ruwa.
Babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin.
An ce harin ya afku ne a birnin Hodeida mai tashar jiragen ruwa da ke kudancin tekun Bahar Maliya, kusa da mashigin Bab el-Mandeb da ke da alaka da mashigin tekun Aden.
Ambrey sun ce Jirgin ya aike da sako ta rediyo, yana mai cewa yankin da yake dakon kaya ya lalace kuma yana daukar ruwa.
