Akalla mutane 20 ne suka Mutu a Sabon Harin da Isra’ila ta kai a Sansanin Rafah


Wani sabon hari da Isra’ila ta kai a wani sansanin tanti da ke yankin da aka kebe na jin kai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza ya kashe Falasdinawa akalla 20.


Harin na yau Talata an kaishi ne a al-Mawasi dake yammacin Rafah, yankin da aka kafa tantuna domin 'yan gudun hijira, in ji kafofin yada labaran Falasdinu.


A baya dai mahukuntan Isra'ila sun shaida wa Falasdinawa fararen hular da aka kama a munanan hare-haren da ta kai a Rafah cewa su guda zuwa kudancin Gaza da ke kan iyaka da Masar domin tsira da rayukansu.


Hukumar tsaron farar hula ta Gaza ta ce wasu tankokin yaki guda hudu sun kai hari kan tarin tantuna a al-Mawasi, inda suka kashe mutane 21, 12 daga cikinsu mata.


 Harin dai ya zo ne kwanaki biyu bayan wani harin da Isra’ila ta kai wanda ya tayar da gobara a wasu tantuna da ke yammacin Rafah, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 45, wanda hakan ya Jawo yin Allah wadai da duniya tayi dasu.


Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da zaman gaggawa a yau Talata domin tattauna halin da ake ciki a Rafah bayan kisan kiyashin da aka yi a ranar Lahadi.


 Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya ta fada a yau Talata cewa sama da Falasdinawa miliyan 1 ne suka tsere daga Rafah tun bayan da sojojin Isra’ila suka mamaye birnin makonni uku da suka gabata.


Post a Comment

Previous Post Next Post