Kisan kiyashin Rafah Shine Zai Ƙara Saurin Rugujewar Isra'ila: Nasrallah


Babban sakataren kungiyar Gwagwarmayar Hizbullah ta Ƙasar Labanon ya yi kakkausar suka kan sabbin kisan kiyashi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, yana mai cewa laifukan da suke yi shi zaya Gaggauta Rugujewar 'yan Mamayar.


Sayyid Hasan Nasrallah a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin a ranar Talata ya ce: "Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta sanar da al'ummar Rafah yankunan da suke cikin aminci, amma sai suka koma kai musu harin bam a wadannan yankuna."


Ya kara da cewa "Laifi na kisan kiyashin da aka yi wa 'yan gudun hijirar Falasdinawa a Gaza yana nuni ne da irin zalunci, son zuciya da kuma tsoron Gwamnatin 'yan mamayar."


Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hari kan wani tanti da ke yammacin Rafah a ranar Talata, inda suka kashe Falasdinawa akalla 21. Harin dai ya zo ne kwanaki biyu bayan wani harin da Isra'ila ta kai wanda ya tayar da gobara a wani tantuna da ke Rafah tare da kashe Falasdinawa da dama da suka hada da kananan yara.


Sayyid Nasrallah ya ce dole ne mugayen laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta aikata ya farkar da kasashen duniya daga sakaci.


Shugaban na Hizbullah ya jaddada cewa sabon kisan kiyashi da aka yi a Rafah ya kawar da duk wani abin rufe fuska da gwamnatin mamaya ta sanya a fuskarta na nuna kanta a matsayin "wayayya".


"Ban ga wata makoma ga wannan gwamnatin ta NAZI ba a wannan yankin," in ji shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post