Mukaddashin shugaban kasar Iran Muhammad Mokhber ya jaddada bukatar bunkasa hadin gwiwar tattalin Arziki da kasar Saudiyya
Duk da adawar da wasu manyan kasashen duniya ke yi, a yau dangantakarmu tana a mataki mai kyau, kuma yankin na matukar bukatar fadada wannan alaƙar, don haka ya kamata kasashen biyu su samu damar yin hakan ta hanyar kara huldar tattalin arziki da kawar da cikas musamman ga kamfanoni masu zaman kansu na kasashen biyu, da kuma biyan bukatun juna. Don tallafawa, ingantawa da daidaita dangantakar siyasa fiye da kowane lokaci.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da aka yi a yammacin yau (Jumma'a), Mohammad Bin Salman ya kuma jajanta akan shahadar Ayatullah Raisi ya kuma bayyana cewa: Lamarin da ya faru ya yi mana zafi sosai. "Rashin Mista Raisi ya cutar da mu baki daya, kuma rashin ministan harkokin wajen Iran, wanda ke da abokantaka da ministan harkokin wajenmu, abu ne mai matukar ciwo"
