Taher Al-Nono wani jami'in Hamas kuma mai ba da shawara ga shugaban Hamas Ismail Haniyeh ya ce Benjamin Netanyahu shi ne mutumin da ke kawo cikas ga shirin sulhu da yarjejeniyar musayar fursunoni a cikin yakin da ake yi a zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labarai na Shehab ya nakalto Al-Nono yana cewa Rafah mashigar Masar da Falasdinu ce kuma kasancewar wasu bangarorin a gurin ba abin yarda ba ne.
Ya kara da cewa mun amince da shirin tsagaita bude wuta da aka yi, saboda ya dace da mafi karancin bukatun al'ummar Palasdinu.
Babban jami'in kungiyar Hamas,Mahmoud al-Mardawi ya bayyana cewa hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawan ke yi a Rafah na da nufin mika wuya ga Falasdinawa da karbar kudin fansa daga hannunsu.
Kungiyar gwagwarmayar Hamas ta Falasdinu a cikin wata sanarwa da ta fitar ta yi Allah wadai da harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a gabashin birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza, tare da daukar hakan a matsayin wata manuniya da ke nuna aniyar gwamnatin kasar na dakile yuwuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu.
Fiye da rabin al'ummar Gaza, kimanin mutane miliyan 1.4, yawancinsu sun riga sun yi gudun hijira daga arewaci sun makale a Rafah.
Dakarun mamaya na Isra'ila sun kaddamar da farmakin, inda suka fara mamaye yankin Gaza na mashigar Rafah da Masar, sa'o'i kadan bayan kungiyar gwagwarmayar Hamas ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Masar da Qatar suka gabatar.
