Mataimakin kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa mutane 80,000 ne suka rasa matsugunansu daga Rafah tun bayan fara farmakin sojojin Isra'ila.
Farhan Haq, mataimakin kakakin majalisar dinkin duniya ya kara da cewa a ranar Alhamis da ta gabata agogon kasar, ofishin kula da ayyukan jin kai na OCHA ya bayar da rahoton cewa, tun a ranar Talata, lokacin da sojojin Isra'ila suka fara kai farmakin kasa a Rafah, kimanin mutane 80,000 ne suka rasa matsugunansu.
Ya kara da cewa "Yawancin wadannan mutanen da suka rasa matsugunansu suna neman tsira ne a Khan Yunis da Deir al-Balah."
Haq ya yi nuni da cewa wadannan yankunan ba su da abubuwan da ake bukata don tallafawa fararen hula da ke bukatar abinci, matsuguni da kuma kiwon lafiya.
Farhan Haq ya ci gaba da cewa, "Babu wani agajin jin kai - ko man fetur na ayyukan agajin da muke gudanarwa - da ya samu shiga ta mashigar Rafah a 'yan kwanakin nan."
Mataimakin kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya ce hukumar samar da abinci ta duniya WFP ta bayar da rahoton cewa a yanzu ba a iya shiga babban rumbun ajiyarta a Gaza.
