Yaman ta tabbatar da kakkabo jirgin da Amurka ta kera


Kasar Yemen ta tabbatar da cewa dakarunta sun yi nasarar kakkabo jirgin saman MQ-9 da Amurka ta kera a kasar Larabawa.

Tashar talabijin ta Al Masirah, babbar kafar yada labarai ta talabijin da kungiyar gwagwarmayar Ansrarullah ta kasar Yemen, ta bayar da rahoton a safiyar jiya Asabar cewa, "Dakarun tsaron saman kasar sun yi nasarar kakkabo jirgin sama samfurin MQ-9 na Amurka a lardin Sa'adah."

A wani ci gaba mai alaka da shi, Ansrarullah sun fada a jiya Asabar cewa makamin nasu ya afkawa jirgin ruwan dakon mai na Andromeda Star a tekun Bahar Maliya, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito.

Kakakin rundunar sojin Yahya Saree ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, an gudanar da wannan jerin hare-hare ne domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da ake zalunta.

A ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ne gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta kai wani kazamin yaki a zirin Gaza da aka yiwa kawanya. Hakan ya biyo bayan farmakin ramuwar gayya da kungiyar gwagwarmayar Palastinu ta Hamas ta kai wanda ba a taba ganin irinsa ba a kan 'yan mamayar a matsayin ramuwar gayya kan yadda take muzgunawa al'ummar Palastinu. Lamarin duk ya faru ne a ranar ta 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kakabawa yankin na Gaza wanda keda yawan jama'a a inda ta katse man fetur, wutar lantarki, abinci da ruwa ga Falasdinawa sama da miliyan biyu da ke zaune a wurin.

Gwamnatin dai ba wai kawai ta gaza durkusar da juriyar Palasdinawa a fagen daga ba, har ma tana shan kashi bisa manyan tsare-tsare a daidai lokacin da kasashen duniya ke nuna bacin ransu kan yakin da suke yi na kisan kare dangi a Gaza.

Post a Comment

Previous Post Next Post