IRNA ta ruwaito cewa Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta tabbatar da shahadar daya daga cikin mambobinta a harin da gwamnatin sahyoniyawa ta kai a kudancin kasar ta Lebanon.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ahed News cewa, a safiyar yau Asabar kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa “Farajollah Ali Hammoud” dan kungiyar Hizbullah wanda kuma ake wa lakabi da “Sajid” ya yi shahada.
Ya kasance daya daga cikin mazauna gundumar "Kfarkela" a kudancin kasar Lebanon, wanda ya yi shahada a harin bam da gwamnatin sahyoniya ta kai a kudancin kasar Lebanon.
A halin da ake ciki kuma, a ranar Juma'a, wasu kwamandojin Al-Jama'ah Al-Islamiyah na kasar Labanon sun yi shahada a harin da gwamnatin sahyoniyawa ta kai.
A cikin wannan harin sojojin gwamnatin sahyoniyawan sun kai hari kan wata motar farar hula a kan hanyar Midoun da ke kudancin kasar Lebanon, sakamakon harin wasu kwamandojin dakarun Fajr na reshen soja na Jama'atu Islamiyya na kasar Labanon masu suna Musab da Bilal Khalaf sun yi shahada.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Mayadeen a yammacin jiya Juma’a cewa gwamnatin sahyoniyawan ta kai hari kan wata motar farar hula a yammacin Bekaa da ke gabashin kasar Labanon da wani jirgi mara matuki.
