Amurka: Babu Canji akan Tallafin Soja da Take ba Isra’ila duk da Kisan Rafah


A wani mataki na nuna goyon baya ga "ci gaba da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi kan zirin Gaza da aka yi wa kawanya, gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta yi nuni da cewa hare-haren da Isra'ila ta kai kan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a kudancin birnin Rafah, bai ketare "jan layi" ba kuma ba zai haifar da canji a manufofin Washington game da Tel Aviv ba.


A cikin jawaban manema labarai a ranar Talata, jami'an gwamnati da dama sun bayyana kisan kiyashin "Isra'ila" da aka yi a Rafah a matsayin "mai raɗaɗi" amma sun yi iƙirarin cewa harin wanda ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa da dama, hari ne ta sama kuma wannan ba wani babban farmaki ba ne.


A cewar Kakakin fadar White House John Kirby ya shaidawa manema labarai "Ba mu tunanin ya kamata Isra'ila ta tura dakaru masu yawa a cikin Rafah a yanzu. Ba ma son ganin wani gagarumin farmakin soja a cikin birnin, kuma har ya zuwa yanzu hakan bai faru ba".


"Sakamakon wannan harin na ranar Lahadi, ba ni da wani canje-canjen manufofin da zan yi magana akan shi," Kirby ya kara da cewa. “Ya faru ne kawai. ‘Isra’ilawa’ za su bincika. Za mu yi sha'awar abin da suka samu a cikin binciken. Kuma za mu ga inda abin ya dosa daga can."


Kakakin fadar White House ya ce, mafi kyawun sakamako shi ne idan ba a samu wani farar hula da aka jima rauni ko kuma aka kashe ba a hare haren soji, amma kuma ya san cewa ba zai yiwu ba a koyaushe a guje wa cutar da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a rudanin yaki.


 "Babu takamaiman adadin mutuwar farar hula da zai sa mu yi wani abu. Muna so mu guji cutar da kowa". Inji shi lokacin da ake tambayar shi adadin mutanen da suka rasa Rayukansu 


"Duk da cewa fadar White House tana tsananin goyon bayan Isra'ila tsawon watanni 8 da suka gabata, amma suna da'awar cewa sun gargadi Isra'ila game da tura sojojinta zuwa Rafah ba tare da wani shiri na kare fararen hula ba".


A ranar Talata, yayin wani taron manema labarai, wani jami'in Pentagon ya ce harin da aka kai ta sama a ranar Lahadi, wanda shi ne mafi muni a Rafah, bai kai abin da fadar White House ta yi gargadi a kai ba.


"Har yanzu abinda ke faruwa a Rafah kimarmu ce, kuma abin da sojojin Isra'ila suke yi, yana da iyaka." Inji Mataimakiyar sakatariyar yada labaran Pentagon Sabrina Singh inda take shaidawa manema labarai.

Post a Comment

Previous Post Next Post