'Yan sandan Faransa sun kama wani mutum a karamin ofishin jakadancin Iran


Daga Shafin IRNA

Wata majiya mai tushe ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa 'yan sandan Faransa sun kama wani mutum da ya yi barazanar tarwatsa kansa a karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris.

A cewar kamfanin dillancin labaran reuters, wata majiyar ‘yan sanda ta shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa an ga mutumin da misalin karfe 11 na safe agogon kasar yana shiga ofishin jakadancin, dauke da wani abu kamar gurneti da bama-bamai. ‘Yan sanda sun killace wurin.

“Daga baya mutumin ya fice daga ofishi jakadancin, kuma da aka bincika aka gano cewa ba ya dauke da bama-bamai,” kamar yadda majiyar ‘yan sandan ta bayyana.

Fassarawa Daga Nasir Hassan Kankia

Post a Comment

Previous Post Next Post