Daga Shafin IRNA
Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amirabdollahian da takwaransa na Turkiyya Hakan Fidan a wata tattaunawa ta wayar tarho sun tattauna batutuwan baya-bayan nan a yankin tare da jaddada bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza.
Bangarorin biyu sun tattauna batutuwan baya-bayan nan a yankin da kuma bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza.
A yayin tattaunawa kan yakin da ake yi a Gaza da kuma rikicin yankin, ministan harkokin wajen Turkiyya ya jaddada bukatar hadin gwiwa wajen kawo karshen rikicin yankin, yayin da ya kuma soki kalaman tunzura jama'a da jami'an Isra'ila suka yi.
Fassarawa Daga Nasir Hassan Kankia
