
Tun da safiyar yau Juma'a ne mayakan Islama na kasar Labanon suka kai hari kan sansanonin sojojin yahudawan sahyoniya har sau biyar.
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da wata sanarwa da ke nuna goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu a Gaza. A cewar sanarwar, mayakan gwagwarmayar Islama na kungiyar sun lalata kayayyakin leken asiri na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke Shabaa ta hanyar amfani da makaman da suka dace. Hakan ya farune domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu dake a Gaza.
A baya-bayan nan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fitar da wasu bayanai guda hudu game da hare-haren makamai masu linzami da suka harba kan sansanonin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila. Hare-haren sun auna sojojin gwamnatin da kayan leken asiri a sansanonin "Bayad Belida", "Roisat Al Alam", da "Al Raheb".