A wata ganawa da ya yi da takwaransa na kasar Aljeriya, ministan harkokin wajen Iran Hossein Amirabdollahian ya yaba da rawar da Aljeriya ke takawa wajen kawo karshen kisan kiyashin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a Gaza.
Amirabdollahian ya gana da ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Ahmed Attaf a jiya Juma'a agogon kasar, a ci gaba da shawarwarin diflomasiyya a birnin New York, inda suka tattauna tare da yin musayar ra'ayi kan sabbin cigaban shiyya-shiyya da na kasa da kasa da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Ministan harkokin wajen na Iran ya yaba da irin karramawar da Aljeriya ta yi wa shugaban kasar Iran a ziyarar da ya kai kasar domin halartar taron kolin iskar gas na kungiyar OPEC da kuma tarukan kasashen biyu, ministan harkokin wajen na Iran ya yi kira da a kara tuntuba da karfafa hadin gwiwa domin tabbatar da tsaro a yankin.
Amirabdollahian ya yaba da irin rawar da Aljeriya ke takawa wajen ganin an kawo karshen kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniyawan ke yi a Gaza, tare da gabatar da kudurin zama mambobin Palasdinawa ga Majalisar Dinkin Duniya, ya kuma yi kakkausar suka kan matakin rashin da'a da Amurka ta yi na kin amincewa da wannan kudiri.
Ya kuma jaddada aniyar Iran na kyautata alaka a siyasance, tattalin arziki da al'adu da aiwatar da yarjejeniyoyin kasashen biyu.
Har ila yau ministan harkokin wajen kasar Aljeriya ya bayyana jin dadinsa da wannan ganawa tare da jaddada muhimmancin fadada alakar kasarsa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a dukkanin matakai na siyasa, tattalin arziki da al'adu.
