A yayin ziyararsa ta diflomasiyya a birnin New York, Amirabdollahian ya gana da Tor Wennesland, jami'in gudanarwa na musamman kan shirin zaman lafiya na yankin Gabas ta Tsakiya (UNSCO), inda suka tattauna abubuwan da ke faruwa a yankin.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, Iran na da 'yancin kare kanta bisa tsarin halaltacciyar kariya da dokokin kasa da kasa. Ya kara da cewa Iran ta kai wani gagarumin harin ramuwar gayya kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, sai dai kawai ta kai hari kan wuraren sojoji da suka kai hari kan karamin ofishin jakadancin Iran a Siriya.
Babban abin da zai taimaka wajen dawo da kwanciyar hankali da tsaro a yankin shi ne dakatar da laifukan da Isra'ila ke yi a zirin Gaza da gabar yammacin kogin Jordan da kuma tsagaita bude wuta mai dorewa a yankin.
A nasa bangaren, Wennesland, ya yi gargadi kan yadda tashe-tashen hankula ke barkewa a yankin, yana mai cewa lamarin ya wuce gona da Iri, kuma al'ummar Palasdinu na rayuwa cikin mawuyacin Hali.
Ya ce dole ne kasashen duniya su mai da hankali kan shirin tsagaita wuta nan take a zirin Gaza.
