An Kunna Tsarin Tsaron Sararin Samaniya a Birnin Isfahan na Kasar Iran, Bayan Jin Qarar Fashewar wani Abu a yankin

 


Isfahan, IRNA - Iran ta kunna tsarin tsaron sararin samaniya da sanyin safiyar Juma'a bayan karar fashewar wani abu da aka ji a kusa da wani babban sansanin sojin sama a lardin Isfahan na tsakiyar kasar, in ji wani jami'in Iran.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar Iran tana cewa fashewar ta sa aka kunna na'urorin tsaron sararin samaniya.

CNN ta kuma yi ikirarin cewa akalla jirage takwas ne suka canza hanyarsu a sararin samaniya a kan Iran.

Ban da haka kuma, tashar CBS ta nakalto wasu jami'an Amurka da ba a bayyana sunayensu ba na cewa gwamnatin Isra'ila ta kai hari a kalla makami mai linzami kan Iran da sanyin safiyar Juma'a.

Sai dai wani babban jami'in sojan kasar Iran a birnin Isfahan, ya yi karin haske kan rahotannin da kuma jita-jitar kafofin yada labarai na yammacin duniya kan wata kara mai karfi da karfe 4 na safe agogon kasar.

Dakarun tsaron saman birnin sun harba wani abu da ake zargi a gabashin Isfahan, lamarin da ya haifar da kara mai karfi, a cewar Birgediya Janar Siavash Mihandoost.

Ba a samu asarar rayuka ba a lamarin, kuma binciken da wani wakilin IRNA ya gudanar ya nuna cewa birnin na Isfahan na cikin yanayi na yau da kullum.

Post a Comment

Previous Post Next Post