Babban sakataren kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu Ziyad al-Nakhalah ya bayyana cewa, zai yi alkawarin cewa babbar nasara ta al'ummar Palastinu ce, kuma nasarar tana kusa.
A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amirabdollahian a yau Asabar a birnin Tehran, Al-Nakhalah ya bayyana cewa, aikin diflomasiyyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya taka rawar gani sosai wajen bayyana matsayin gwagwarmayar Palastinawa da goyon bayanta, kuma hakan yana da matukar muhimmanci.
Karin Labarai
Damascus ta Bukaci Amurka da ta kawo karshen Haramtaccen Zamanta a kasar Siriya
"Mun san cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta tsaya tsayin daka kan gwagwarmayar Palastinawa tun farkon juyin juya halin Musulunci, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu, wanda hakan yasa aka kakabawa Iran takunkumi da dama don tauye haqqin Palasdinawa," in ji Sakatare Janar na Harkar Jihad Islami na Falasdinu.
Ya yi nuni da cewa, Iran ita ce mai goyon bayan al'ummar Palastinu, kuma da ba don goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, da Palasdinu ba za ta iya ci gaba da zama lafiya ba a guguwar Al-Aqsa ba.
Amirabdollahian da al-Nakhalah a wata ganawa da suka yi a birnin Tehran a jiya Asabar sun tattauna kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
