Damascus ta Bukaci Amurka da ta kawo karshen Haramtaccen Zamanta a kasar Siriya

Damascus



Kasar Syria ta yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri na baya-bayan nan da sojojin mamaya na Amurka suka kai, inda suka kai hari a wasu yankuna na lardin Dayr Al-Zawr da ke gabashin kasar, lamarin da ya janyo hasarar rayuka.

Ma'aikatar harkokin wajen Syria ta fada a ranar Talata cewa Amurka tana daukar kanta a matsayin 'yar sandan duniya yayin da take keta dokokin kasa da kasa da kuma dokokin Jin kai na kasa da kasa.

Ta jaddada cewa, dole ne Washington ta kawo karshen haramtaccen zamanta a kasar ta Siriya, sannan ta kawo karshen goyon bayan da take ba wa kungiyoyin ta'addanci irinsu Daesh.

A yayin da take kira da a dauki matakin da ya dace a daukacin duniya domin dakile ayyukan ta'addancin Amurka a yammacin Asiya, Syria ta sha alwashin gurfanar da masu ta'addancin a gaban kotu kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.

Majiyar sojin Syria ta ce hare-haren na Amurka sun kai hari a kauyuka da garuruwa da wuraren soji.

Sun kashe sojoji 7 da farar hula daya yayin da suka jikkata sojoji 19 da fararen hula 13.
Amurka na kai hare-hare ta sama a Syria akan cewa tana yaki da 'yan ta'adda.

Damascus ta rubuta wasiku da dama ga Majalisar Dinkin Duniya, inda ta yi kira ga 
kasashen duniya da su kawo karshen hare-haren da Amurka ke kai wa a kasa.

Dakarun mamayar na Amurka sun kai wasu jerin hare-hare ta sama kan wasu wurare a gabashin Syria, kusa da kan iyaka da Iraki.

Gwamnatin Syria ta ce Isra’ila da kawayenta na kasashen yamma da na shiyya-shiyya suna goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’addan takfiriyya domin ci gaba da barna a duk fadin kasar tun a watan Maris din shekarar 2011, lokacin da kasar ta fada cikin halin ‘yan ta’adda da ke samun goyon bayan kasashen waje.

Amurka ta girke sojoji da kayan yaki a arewa maso gabashin Syria.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi ikirarin tura sojojin da nufin hana rijiyoyin mai da ke yankin fadawa hannun 'yan ta'addan Daesh.

Sai dai Damascus tace tura sojojin na da nufin wawashe albarkatun kasar ta Syria.

Post a Comment

Previous Post Next Post