Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a biya diyya kan fataucin bayi da akeyi zuwa kasashen ketare a matsayin wata hanya ta tinkarar abin da aka gada a cikin al'ummar yau, gami da wariyar launin fata.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ta bikin Ranar tunawa da wadanda aka Bautar da kuma Cinikin bayi da ake yi a yankin tekun Atlantika, Guterres ya ce bautar ya kafa tushen tsarin nuna wariya wanda ya danganta hakan ga farar fata da har yanzu ake ci gaba da yi.
"Muna kira da a samar da tsarin shari'a na gyara don taimakawa wajen shawo kan wariya." in ji Guterres.
Daga karni na 15 zuwa na 19, an kwashi a kalla 'yan Afirka miliyan 12.5, a jiragen ruwan 'yan kasuwan Turai da karfi, inda aka sayar da su a matsayin bayi. Waɗanda suka Rayu daga cikin su sun ƙare a aikin gonakin Amurkawa, galibi a Brazil da Caribbean.
"Da yawa daga cikin wadanda suka shirya da gudanar da cinikin bayi sun tara dukiya mai yawa. Wanda an hana bayin samun ilimi, kiwon lafiya, dama wadata," in ji babban jami'in MDD.
A cewar Guterres, rayukan wadanda suka fada cikin bautar ‘yan ta’adda ne, saboda ana yi musu fyade, bulala, sara, da sauran cin zarafi da wulakanci.
"Kuma mun yanke shawarar yin aiki domin samar da duniya da ba ta da wariyar launin fata, son zuciya da kuma ƙiyayya," in ji shi.
A Ranar litinin, shugaban babban taron na MDD Dennis Francis ya kuma bayyana irin balaguron da miliyoyin mutane suka sha a lokacin, tare da kawar da sunayensu da mutuncinsu.
"Ba za a iya tunanin cewa an yi wa bayin zalunci ba yadda aka daukesu a matsayin kayayyaki kawai na siyarwa da cin gajiyar su," in ji Francis.
Ya kara da cewa, "tare da 'ya'yansu da aka haifa a cikin bauta,"
Francis ya kuma yi kira da abada Diyya a matsayin adalci na gaskiya, yana mai jaddada bukatar gaggawa na magance wariyar launin fata da al'ummar Afirka ke fuskanta, na tarihi da na zamani.
"Ya zama wajibi a kan jihohi, cibiyoyi, da daidaikun mutane su amince da rawar da suka taka wajen ci gaba da dawwamar wadannan abubuwan da suka gada na rashin adalci, kuma su dauki matakai masu ma'ana don samar da adalci," in ji shi.
A watan Satumban da ya gabata, wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya ba da shawarar cewa ya kamata kasashe su yi tunanin Diyya a matsayin hanyar magance rashin adalci na bautarwa.
Manufar diyya ga bauta ta hanyar ramuwa ko wasu nau'ikan ramawa tana da dogon tarihi, kuma a halin yanzu tana samun karbuwa sosai a duniya.
Hilary Beckles, shugabar hukumar ramuwa ta kungiyar siyasa da tattalin arzikin yankin Caribbean (CARICOM), ta fada a babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa, "Wannan shi ne yunkurin da zai nuna, nasarar da dan'adam ya samu, na alheri a kan mugunta."
An kafa hukumar ta CARICOM don biyan diyya, wanda zai iya haɗawa da gafarar bashi da taimako wajen magance matsalolin lafiyar jama'a, daga tsoffin turawan mulkin mallaka kamar Ingila, Faransa, da Portugal.
Lokaci ya yi da "Birtaniya da sauran 'yan mulkin mallaka na farko da na yanzu za su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu," in ji Verene Shepherd, darektan Cibiyar Binciken Gyara a Jami'ar West Indies.
