TUNAWA DA SHAHADAR SAYYIDA ZAHRA (AS) 3

 YAA MAHDI 

ABUBUWAN DA ZAMU KAWO YAU SUNE

-Wani Kusurwa Da Sharar Fagen Saqifah: Rashin Imam ‘ali Da Bani Hashim

-Jawabin Imam Ali

-Harin Gidan Imam Ali Da Jawabin Sayyidah Zahra

--Abin Da Ya Faru Na Tilasta Mubaya’a Ga Imam ‘Ali A Fad'in Maluman Ahlus Sunnana

WANI KUSURWA DA SHARAR FAGEN SAQIFAH: RASHIN IMAM ‘ALI DA BANI HASHIM

Fitaccen malamin nan, Shaikhul Mufid ya fada a cikin littafinsa al-Irshad cewa, “Bayan wafatin Annabi Imam Ali ya shagaltu da wanka da tufa da jana’izar (Annabi), alhali Bani Hashim sun nisanta kansu daga jama'a saboda wannan babban bala'i.  Don haka ne mutane suka yi amfani da wannan damar dangane da halifanci da zabar halifa, suka kafa shugabancin Khalifa na farko ba tare da Imam Ali da Bani Hashim ba.

 A yayin da aka samu sabani tsakanin Ansaru dangane da wannan lamari, wadanda aka 'yanta (a lokacin cin nasarar Makkah) da wadanda Manzon Allah ya ba su izinin shiga Musulunci don su canza zukatansu, sun kyamaci duk wani jinkiri da aka samu wajen zaben halifa. Don haka suka daidaita al’amarin halifanci, suka yi wa Khalifa na farko mubaya’a, kafin Bani Hashim su kammala.  Sun yi haka ne saboda Khalifa na farko ya kasance a wurin taron (Saqifah) kuma abubuwa da sharuddan sha’aninsa sun kasance a shirye kuma abin karva ne”.

Ba za mu kawo cikakkun bayanai game da wannan lamari a cikin wannan littafi ba, amma za mu bar shi zuwa wani littafi.

JAWABIN IMAM ALI

 An ruwaito cewa, a lokacin da aka kammala bai’a ga Khalifa na farko, wani mutum ya zo wurin Imam ‘Ali a lokacin Imam yana dauke da Shebur ya shagaltu da shirya kabarin Manzon Allah.  Ya ce wa Imam Ali: “Mutane sun yi mubaya’a ga Khalifa na farko, alhali kuwa Ansar sun sha kashi a kan wannan al’amari na zabar halifa, saboda sabani ya taso a tsakaninsu.  Wadanda aka ‘yanta (waɗanda Annabi ya ‘yanta su a lokacin cin nasarar Makka) sun riga sun yi mubaya’a gare shi (Khalifa na farko), ba su nemi shawararka ba saboda ba ka nan.”

Sai Imam Ali ya ajiye shebur a lokacin da marikinsa ke hannunsa, ya ce;

 “Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai. A. L̃. M̃. .  Ashe, mutãne sun yi zaton a bar su su ce: ''Mun yi ĩmãni,'' alhãli kuwa bã zã a fitine su ba?''  Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabãninsu, dõmin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata. , Kõ waɗanda ke aikata miyãgun ayyuka sun yi zaton su tsẽre Mana? Abin da suke hukuntãwa ya mũnana. "

HARIN GIDAN IMAM ALI DA JAWABIN SAYYIDAH ZAHRA

 ‘Allamah al-Tabarsi, mawallafin al-Ihtijaj ya ruwaito daga Abdullahi b.  'Abdul Rahman b. Awf, "Wane ya d'aure rigarsa a kugu, ya zaga cikin birnin Madina yana kira da cewa, ‘Mutane sun yi mubaya’a ga Wane, don haka ku gaggauta yin haka!’ Mutane ba su da wani zabi face yin mubaya’a ga Wane.  Sai aka gayawa Wane (mai kiran mutane suyi mubaya'a) cewa wasu jama’a sun boye kansu a cikin gidajensu don haka tare da rakiyar wasu mutane ya far musu ya kawo su Masallaci ya tilasta musu yin mubaya’a a hannun Khalifa.

Bayan Wasu kwanaki sai Wane ya zo gidan Imam Ali tare da rakiyar mutane, Ya kira Imam ‘Ali da ya fito daga gidansa (ya yi bai’a).  Imam Ali ya ki yin haka.  Sai Wane ya 'kira itace da wuta ya ce: ‘Na rantse da wanda ran Wane (Shi ya fadi Sunan sa ne)  ke hannunsa!  Idan bai fito ba (yana nufin Imam ‘Ali), zan banka wa gidan wuta tare da wadanda ke cikinsa.

Wasu daga cikin wadanda ke wurin sun shaida wa 'Wane' cewa: “Fatimah ‘yar Annabi tana cikin gidan da ‘ya’yansa (Imam Hasan da Imam Husaini) da alamominsa.” Sai mutane suka fara nuna adawa da Wane (da barazanar qona Gida) da ya gane tsananin al’amarin, sai ya ce, ‘Me kuke tunani?  Kuna tsammanin zan yi haka da gaske?  Ni dai ina nufin in tsorata su ne ba kona su ba.

 Imam Ali ya aiko da sako yana mai cewa, ‘Ba zai yiwu in fita waje ba, domin ina shagaltuwa da harhada Al-Qur’ani da kuka yi watsi dashi a bayanku, kuna jingina kanku da son abin duniya.  Na yi rantsuwa cewa ba zan fita daga gida ba, kuma ba zan sa alkyabbata ba har sai na gama hada Alkur’ani.

A nan take Fatima ‘yar Manzon Allah ta fito ta tsaya kusa da kofa tana fuskantar mutane ta ce, ‘Ban san wata kungiya da ta fi ku rashin tarbiyya ba!  Kun bar gawar Annabi a tsakiyarmu kun dauki al'amuran (zabar halifa) a hannunku!  Ba ku nemi shawararmu ba, maimakon haka, kun yi watsi da hakkinmu. Watakila ka yi kamar ba ka san lamarin Ghadir ba.  Wallahi! A wannan ranar, Manzon Allah (Saww) ya riki alqawarin mutane game da abota da Jagorancin Ali. Manzon Allah (Saww) ya yi haka ne don kada ku yi Sha'awar d'aukar Jagoranci a hannunku, amma kuka soke alaqar ku da Annabi (da yin haka).  Lallai Allah ne mai hukunci tsakaninmu da ku a duniya da lahira.”

ABIN DA YA FARU NA TILASTA MUBAYA’A GA IMAM ‘ALI A FAD'IN MALUMAN AHLUS SUNNA.

Mubaya'a a wajen Ibn Qutaybah al-Daynuri

 Abu Muhammad Abdullahi b.  Muslim b.  Qutaybah al-Daynuri, wanda aka fi sani da Ibn Qutaybah al-Daynuri, mashahurin malamin Ahlus Sunna wanda ya rayu a zamanin “karamin gaiba” (na Imam al-Mahdi) ya rasu a shekara ta 322, ya rubuta a cikin littafinsa al-Imamah was-siyasah dangane da kin amincewar da Imam Ali ya yi wa 'Wane' cewa, “Sai aka zo da Ali (karramal lahu wajhahu) (da qarfi) zuwa ga Khalifa yayin da yake kira da cewa: 'Ni bawan Allah ne kuma dan'uwan Manzon Allah.

 Wani mutum ya ce masa ka yi mubaya'a a hannun halifa, sai ya ce: 'Ni ne mafi cancantar halifanci a kan ka, ba zan yi maka mubaya'a ba, alhali kuwa kai yafi cancantar kayi mubaya'a a hannuna. Yayin da kuka ɗauki matsayi a hannunku!  Kun kwace halifanci daga hannun Ansaru bisa hujjar cewa ku 'yan uwansa ne don haka a haqiqa kun kwaci haqqi daga gare mu - Ahlul Baitin Annabi!  Shin ba ku gabatar da wannan da'awar a gaban Ansar cewa kun fi cancantar ku gaji Muhammadu (saww)  kasancewarku danginsa na kusa ba?  Da haka ne Ansar suka mika maka mulki suka mika wuya.  Yanzu na gabatar da da'awar da kuka yi wa Ansaru (dangane da alakar Annabi). Na fi kusanci da Annabi a rayuwarsa da kuma a yanzu bayan wafatinsa. To, ku yi mana adalci idan kun kasance kunada imani, ko kuwa kun nemi tsira da gangan don zalunci.

 Sai Wane ya ce: “Ba za mu sake ka ba har sai ka yi bai’a ga Halifa.

 Jin haka sai Imam Ali ya ce: “Ka sha madara, ka ajiye rabi, ka yi jihadi a gare shi (Watau ga Halifa) a yau, domin gobe zai mayar maka da ita (Khalifancin).” Sa’an nan ya ci gaba da cewa: “Ya kai” Wane!  Wallahi!  Ba zan yarda da maganarka ba, in yi masa bai’a.” Sai Khalifa ya ce: “Idan ba ka yi mubaya’a ba, ba zan tilasta ka ba.

 Sai Abu Ubaidah al-Jarrah ya ce, ‘Ya kai dan uwa!  Kai har yanzu matashi ne alhalin su biyun nan manya ne a cikin al’umma kuma ba ka da irin gogewa da hankali da suke da shi.  Ni a ra’ayina Wane ya fi ka Ikon daukar nauyin halifanci a hannunsa, kasancewar ya fi ka haquri, kuma ya fi ka ilimi.  ka Miqa Halifanci ga Wane Idan kayi tsawon Rai ka kasance Raye, Sai kazama mai hakki na halifanci dangane da fifiko, addini, ilimi, hankali, girma, dangantaka da kyautatawa da ka mallaka.

 Sai Imam Ali ya ce: “Allah!  Allah!  Ya Muhajirun!  Kada ku fitar da ‘Ikon Annabi a cikin ‘Larabawa daga cikin gidansa zuwa ciki da kasan gidajenku!  Ku kare matsayin Ahlulbaitinsa a tsakanin mutane da hakkokinsu!  Ya ku Muhajirun!  Wallahi!  Mu ne mafi cancanta a cikin dukkan mazaje da mu karbe mulki a hannunmu, domin mu Ahlul Baitin Annabi ne kuma mun fi kowa cancantar halifanci.”

NEMAN TAIMAKO DAGA ANSAR

 Ibn Qutaybah ya ci gaba da cewa: “Da dare Ali (Karramal-lahu wajhahu) ya zaunar da Fatima a kan wani Abin hawa ya kai ta wurin Ansar, ta ce su goyi bayan Ali.  Suka ce: ‘Ya ‘yar Manzon Allah!  Mun yi mubaya'a ga wannan mutumin (Wane) bakin Alqalami ya bushe.  Da a ce dan uwanki kuma mijinki ya same mu tun farko, kafin mu ba da mubaya’a ga Wane, da mun ba shi goyon baya da saurarensa dangane da halifanci.

 ‘Ali ya amsa musu da cewa, ‘In haka ne in bar gawar Annabi a gidansa ba a binne shi ba, in zo wurinku in yi jayayya da maza a kan halifanci?

 Fatimah ta ce: “Abul Hasan (Imam ‘Ali) ya kasance yana yin jana’izar Annabi, a lokacin da Muhajirina da Ansar suke aikata irin wannan aika-aikar da Allah zai tsawatar da su kuma ya azabtar da su.

Ibn Qutaybah ya ruwaito dangane da yadda aka tilasta wa Imam Ali mubaya’a cewa: “Lokacin da aka gayawa Wane labarin wadanda ba su yi masa mubaya’a ba, kuma suna tare da Ali, sai ya aika Wane zuwa gare su.  Sai wane ya je gidan Ali ya kira su da su fito su yi mubaya’a, amma suka ki fitowa.  Sai Wane ya ce: “Na rantse da wanda rai na (Shifa sunan sa yakira nine nace wane)  yake hannunsa!  Lallai ku fito, ko kuwa in kona gidan da mutanen da ke cikinsa.”

 Wasu daga cikin wadanda ke wurin suka ce wa Wane: “Fatimah ma tana cikin gidan”, sai Wane ya ce, “To”.  Don haka duk wadanda suke cikin gidan aka tilastawa fitowa su yi mubaya’a in ban da Ali wanda ya rantse da cewa: “Ba zan fito daga gidana ba, kuma ba zan sa riga a kafadata ba har sai na kammala hada Alkur’ani.  .”

Fatimah ta tsaya kusa da kofa ta yi wa Muhajirun magana tana cewa, “Ban san wata kungiya da ta fi ku rashin tarbiyya ba, kun bar gawar Annabi a tsakaninmu, kuka dauki al’amura a hannunku, ba ku nemi shawararmu ba. Kuma kunyi watsi da hakkinmu”.

Da Wane ya ji wannan magana, sai ya je wurin Wane ya ce masa, “Me ya sa ba ka kama wannan mutumin ko ka tsawata masa ba, tunda ya ki yin mubaya’a?

 Wane ya kira Qunfudh, ‘yantaccen bawansa, ya aike shi wurin Ali da saqon cewa (‘Ali) ya je wurin Abubakar.  Qunfudh ya je wurin Ali, ya tambaye shi abin da yake so.  Qunfudh ya karva masa da cewa: “Halifan Manzon Allah yana kiran ka.  Sai Ali ya ce: “Yaya za ka jingina qarya ga Annabi (da cewa Wane ne halifansa)?  Qunfudh ya koma wurin Wane ya gaya mashi amsar Ali, jin haka yasa Wane ya yi kuka mai zafi.

 Wane ya sake maimaita wa wane yana cewa: "Kada ka yi jinkiri ga wannan mai cin zarafin (yana nufin Imam Ali)."  Wane ya ce wa Qunfudh, ka je wurin Ali ka gaya masa cewa Amirul Muminina ya gayyace ka ka zo wurinsa ka yi mubaya’a.  Qunfudh ya koma wurin Ali ya ba shi labarin wane.  ‘Ali ya daga murya ya ce: “Tsarki ya tabbata ga Allah!  Yana da'awar abinda (matsayin) ba nasa ba ne!"  Qunfudh ya koma wurin Wane ya ba shi labarin maganar Ali, ya ji wane ya sake yin kuka mai zafi.

 Nan da nan Wane ya tashi ya raka shi da gungun mutane, ya zo gidan Fatimah ya buga kofa.  Da Fatima ta ji muryarsu, sai ta yi kira da babbar murya ga mahaifinta, “Ya baba!  Ya Manzon Allah!  Wane zalunci ne ya same mu na xan Wane da xan Wane bayan wafatin ka!”.

 Yayin da wadanda ke tare da Wane suka ji muryar Fatima da kukanta, sai suka yi bakin ciki matuka, suka yi kuka mai zafi, har kamar an tsage zukatansu, ana huda musu hanta (saboda tsananin bakin ciki), amma wane ya ci gaba da zama a gidan Fatimah da qarfi ya fito da Ali daga ciki ya kai shi wurin Khalifa ya ce: “Ka Mubaya'a ga Halifa!”

Sai Ali ya ce: "Ba zan yi ba."  Suka ce: “Tallahi!  Idan ba ka yi mubaya’a ba, za mu sare kan ka.”  Sai Ali ya ce: “Haka za ka kashe bawan Allah kuma dan’uwan Manzon Allah.  Sai Umar ya ce: “Bawan Allah – eh, amma dan’uwan Manzon Allah – a’a!”. 

 Halifa ya yi shiru duk wannan lokaci bai ce uffan ba, sai Wane ya ce masa, “Shin ba ka umurci Ali da ya yi mubaya’a ba?”  Sai Halifa ya ce: “Ba zan tilasta wa Ali komai ba, matukar Fatima na tare da shi.

 ’ Ali ya fita ya nufi kabarin Manzon Allah (Saww) yana kuka, ya yi kira da murya mai baqin ciki, ya ce: “Ya xan uwana!  Lalle ne mutãne sun ɗauke ni mai rauni, kuma sun nẽmi su kashe ni."

Zamu cigaba... 

Post a Comment

Previous Post Next Post