Da sunan Allah mai Rahama Mai Jinkai
Ina taya Imamin mu Shugabanmu Sahibul Asr waz zaman (As) da kuma Jagoran mu Sayyid Zakzaky (H) Juyayi na zagayowar wannan Ranaku na Shahadar Sayyida Zahra (As). Ina roqon Allah da yaba Malam Lafiya Kuma ya kareshi daga Sharrin duk wani Mai Sharri.
Ina kuma roqon Allah daya yafe mani kura-kurai na wanda nayi dama wanda zaniyi nan gaba musamman gurin wannan gagarumin Aiki na kawo Abinda ya faru da Shugabar Matan Duniya baki daya Sayyida Zahra (As)
Sannan Inaso inyi jan Hankali ga wadanda wannan shine Farkon jinsu Ga wannan Al'amari da cewa "yakai dan uwa ka sani cewa shi Ilimi Fadi gareshi kuma duk abinda kaji amma baka taba jinshi ba da can to kada kace qarya ake saboda kai ba komai ka sani ba kaje ka bincika shine kawai mafita ba cewa karya ake ba. Wannan Al'amari na Shahadar sayyida Ya faru kuma an rubuta shi saboda haka ni kawai abinda nayi shine fassara, kuma ka sani abinda ban kawo ba yafi wanda zan kawo yawa.
Sannan abubuwan da zani kawo na ciro shi daga cikin Littafin Shehin Malamin nan Sheikh ABBAS QUMMI Rahimahullah ma Rubucin Littafin Mafatihul Jinan. Shi wannan littafi an fassara shi Zuwa turanci Yana da Page 208, kuma ya kawo abubuwa dabab-daban kafin Wafatin manzon Allah dama bayan wafatin Manzon Allah. Ga sunan Littafin (HOUSE OF SORROW, THE LIFE OF SAYYIDAH FATIMAH AL-ZAHRA AND HER GRIEF) Ga mai buqata yana iya shiga website din mu domin ya dauko (Download) shi.
Zamu kawo shi Insha Allah Tun daga Haihuwar ta Har zuwa Sahadar ta, amma ba lokaci guda ba, duk Lokacin da muka gama fassara zamu tura domin kuje ku karanta, kuma saboda idan muka Kawo shi sosai mutum zai gaji da karantawa shi yasa muka ce bari a dinga kawowa kadan kadan. Zaku Iya samun shi ta Website din mu ko kuma a Facebook page din mu wato a Facebook kenan. Kawai kuyi following na website din da kuma Facebook page din mun gode.
ABUBUWAN DA ZAMU KAWO YAU SUNE
1)Haihuwar ta
2)Sunayen ta
HAIHUWARTA
Sheikh As-Saduq ya ruwaito ta hanyar jerin Maruwaita daga Mufadhdhal b. Umar ya ce: “Na tambayi Imam Sadik game da haihuwar Sayyidah Fatimah, sai Imam ya ce: “Lokacin da Khadijah ta auri Manzon Allah, matan Makka (saboda kiyayyarsu da Musulunci) sun nisanta kansu daga gare ta. Ba sa ziyartar gidanta, kuma ba su gaishe da ita, kuma ba su yarda wata mace ta ziyarce ta ba. Don haka Khadijah ta shiga cikin tsananin damuwa, don kada su cutar da Annabi. Amma Lokacin da Khadijah ta samu cikin Fatimah, (Fatimah) takan yi magana da mahaifiyarta tun tana cikin ta, ta kuma yi mata jaje - wani abu da Khadijah ta boye wa Annabi. Watarana Annabi ya shiga gida sai ya ji Khadijah tana magana da wani, sai ya ce: “Wa kike magana da shi?” Khadijah ta ce: ‘Yaron da ke cikina yana magana da ni, kuma abokina ne, sai Annabi ya ci gaba da cewa, ‘Jibra’il. yana sanar dani cewa wannan yaron diya ce, tsarkakkiya kuma kyakkyawa, kuma da sannu Allah zai ninka zuriyyata ta hannunta kuma shugabanni (Imamai) da Allah ya naxa su za su fito daga zuriyarta kuma za a sanya su Khalifofi da kuma magada bayan Karewar wahayi (wato bayan wafatinsa).” 2
Sayyidah Khadijah ta kasance a haka tunda ta samu cikin Sayyidah har zuwa lokacin da naqudah tazo mata. Sai ta aika da sako zuwa ga matan Kuraishawa da Bani Hashim da su taimaka mata wajen haihuwa, kamar yadda mata suke taimakon mai ciki a lokacin haihuwa. Sai dai matan Kuraishawa da Bani Hashim suka amsa da cewa, saboda ba ta kula da maganarsu ba, kuma ta yi watsi da su ta hanyar auren Muhammad marayan Abu Talib (Abdullahi) wanda ba shi da hali, ba za su zo su taimake ta ba, haka nan, ba zasu taimaka mata ta kowace hanya ba. Wannan matsanancin lokacine a farkon kwanakin Da'awarsa! Annabi yana da makiya da yawa kuma Musulunci ya kebanta ta yadda ko a lokacin haihuwa mutane sun nisanta kansu da matar Annabi sun ki taimaka mata!
Khadijah ta rasa natsuwa da bacin rai bayan jin amsarsu, amma Ubangijinta bai yashe ta ba. Nan take taga wasu mata hudu masu launin alkama da tsayi irin na matan Bani Hashim sun shigo dakinta. Kallon su Khadijah ta rude. Nan take daya daga cikinsu tace, “Ya Khadija, kada ki yi bakin ciki! Mun kawo muku agaji da izinin Allah. Mu ’yan’uwanku ne, ni Saratu ce (matar Annabi Ibrahim); Wannan ita ce Asiya, diyar Mazahim (matar Fir'auna), wadda za ta kasance abokiyar zaman ki cikin Aljanna; wannan kuma ita ce Maryam ’yar Imrana; Sai ta hudu Kulthum 'yar uwar Annabi Musa b. "Imran. Allah Ta’ala ya aiko mu ne domin mu taimake ki a lokacin haihuwa”.
Daya daga cikinsu ta zauna a gefen dama na Khadijah, ta biyu a hagunta, ta uku tana fuskantarta, ta hudu a bayan kai. A lokacin ne Sayyidah Fatimah ta iso duniya cikin tsafta da kyawawan dabi'u. Tana kwantawa kasa sai ga wani haske mai haskakawa ya fito daga gare ta ya haska dukkan gidajen Makkah, babu komai a gabas ko yamma, face haskenta mai kyalli ya haskashi.
Nan da nan sai ga Huril'in goma na Aljannah suka sauko, dauke da tire da tuluna cike da ruwan magudanar Al-Kauthar. Matar dake tsaye gaban Khadijah ta daga Fatimah ta wanke ta da ruwan (al-kausar). Sai aka kawo wasu fararan kyalle guda biyu wadanda suka fi madara fari da fitar kamshi fiye da miski da ambar aka nannade ta a daya daga cikinsu, na biyun ya zama shamaki. Daga nan suka bukaci Fatimah tayi magana. Sai ta bude baki ta shaida kadaita Allah da Annabcin Muhammadu a cikin wadannan kalmomi, “Na shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Babana Manzon Allah ne, shugaban Annabawa, kuma Ali shi ne shugaban mataimaka, kuma ‘ya’yana su ne shugabannin kabilu (Asbat).”3
Bayan haka, ta gai da wadannan matan hudu tana kiran su da sunayensu sannan suka bi ta cikin amsawa da murmushi. Huril'in da ‘yan Aljanna sun yi wa juna barka da haihuwar Fatimah, yayin da wani haske mai daraja ya haskaka a kan sammai, irin wanda mala’iku ba su taba ganin irinsa ba.
Sai matan suka juya wajen Khadijah, suka ce, “Ki riki Diyarki mai tsarki, kyakkyawa, mai wadata da jin dadi, kuma zuriya mai albarka za su fita daga gare ta. Khadijah ta rik'o hannunta cike da jin dad'i tana ciyar da ita. Shekarun Fatima yana 'karuwa kowace rana daidai da wata (na sauran yara) kuma kowane wata ya kai shekara daya idan aka kwatanta da sauran yara.
SUNAYENTA
Yunus b. Abiyan ya ruwaito cewa, Imam Ja’afar as-Sadiq ya ce: “Fatimah tana da sunaye tara a wurin Allah: Fatimah, As-Siddiqah, al-Mubarakah, at-Tahirah, az-Zakiyyah, ar-Radhiyyah, al-Mardhiyyah, al-Muhaddatha da kuma al-Zahra." Ya ci gaba da cewa, ka san abin da Fatima ke nufi? Sai na ce: “Ya shugabana, ka ba ni labarinsa”, sai ya ce: “Wanda ya rabu da kowane irin kazanta. Daga nan sai ya ci gaba da cewa, da ba a halicci Amirul Muminina Ali ba, da ba a sami tamka da Fatima a duk fadin duniya ba, tun daga zamanin Adamu har zuwa karshen duniya.
A wasu hadisai an sanya mata suna Fatima saboda za a 'raba ita da shi'ar ta daga wutar jahannama, haka nan kuma saboda ta bambanta da wasu saboda hikimarta da fifikonta, da kuma kasancewarta an kareta daga jinin haila. Ya wuce tunanin dan Adam sanin Fifikon ta, Allah ya nisantar da ita da zuriyarta masu tauhidi da imani, da abokanta daga wutar jahannama. An kuma ruwaito cewa sunanta Fatimah ya samo asali ne daga sunan Allah, ‘al-Fatir’ (wanda ke nufin Mafari).
Ana kiran ta da suna ‘at-Tahirah’ saboda ta tsarkaka daga dukkan kazanta da kuskure kuma ba ta taba ganin jinin haila ko haihuwa ba. Ana kiran ta da suna ‘al-Zahra’ saboda hasken kyawunta yana haskakawa a kullum sau uku ga Amirul Muminina Imam Ali (As). Abu Hashim Ja’fari yana cewa: “Na tambayi Imam Hasan al-Askari dalilin da yasa ake kiran Sayyidah Fatimah ‘al-Zahra’ sai Imam ya amsa masa da cewa, ‘Hasken Sayyidah Fatimah ya haskaka ma Imam Ali a farkon rana, kama da hasken rana; kuma a lokacin farkon maraice kamar wata mai haskakawa; alhali a faɗuwar rana ya yi kama da taurari masu haskakawa.”
Shaikh As-Saduq ya ruwaito daga Imam Ali al-Ridha cewa: “Lokacin da watan Ramadana ya haskaka a sararin samaniya, hasken Sayyidah Zahra ya rinjayi a kansa. hasken wata kuma zai boye shi. Ana iya ganin wata ne kawai lokacin da Fatima ba ta nan.”
Imam Ja’afar As-Sadiq (As) yana cewa, “An sama Fatimah suna al-Zahra ne saboda Allah ya yi mata kubba na jan yakutu a cikin Aljanna. Tsawon kubba yana daidai tazarar shekara guda (na tafiya) kuma an dakatar da shi a cikin iska da ikon Allah, ba tare da an kama shi da sarkoki daga sama ba don kula da shi, kuma babu ginshiƙi daya. Kubbar ta ƙunshi kofofi dubu goma kuma a kan kowace kofa, mala'iku dubu suna tsaye a kan tsaro. ’Yan Aljanna za su ga kubba kamar yadda kuke ganin taurari a sararin sama, sai a ce musu: ‘Wannan kagara (kagara) na Fatima ne.”
An ruwaito a wani hadisi cewa, sau daya Allah Ya so domin ya jarraba mala'ikunSa. Ya aika musu da wani baƙar gajimare wanda ya mayar da sararin duhu, har ba za su iya ganin juna ba. Sai suka roki Allah ya kawar da shi, kuma Allah ya karbi rokonsu, ya halicci hasken Fatimah mai kama da fitila. Allah ya dakatar da ita (fitila) a cikin sammai, har sammai bakwai da ƙassai bakwai suka haskaka da haskenta. Mala’iku sun yi tasbihi ga Allah, kuma ya ce: “Na rantse da girmana da daukaka Na! Lallai ni mai bayar da ladan yabonku da tasbihin ku (Kaina) har zuwa ranar Alkiyama ga abokan Zahra da abokan babanta da mijinta da ’ya’yanta.”
Daga cikin sauran sunayen Sayyidah Zahra akwai: al-Hisan, al-Hurrah, as-sayidah, al-Azra', al-Hawra', Maryam al-Kubra da al-Batul. An ruwaito ana kiran ta da ‘al-Batul’ saboda ba ta taba ganin jinin haila ba; haka kuma Maryam, mahaifiyar Annabi Isa (Yesu) ita ma ana kiranta da al-Batul. Wasu malaman sun ruwaito cewa sunanta 'al-Batul' ya samo asali ne daga 'Batal' (wato ta rabu), kuma yana nufin ita ta nisanta daga duniya, kuma ta nemi kusanci zuwa ga Allah; yayin da wasu ke cewa an sa mata sunan ne saboda ba ta da tamka kuma babu kamarta.
Ibn Shahr Ashub ya fada a cikin littafinsa al-Manaqib cewa, “An ruwaito ta hanyar ruwayoyi amintattu cewa Sayyidah Fatimah tana da sunaye ashirin, kuma kowanne daga cikin sunayenta ya zo da daya daga cikin kamalarta”, kuma Ibn Babawayh ya kawo wadannan sunayen a cikin littafinsa. Mawlid Fatimah.
Al-Kunyah (lakabinta) sun zo kamar haka: Ummul Hasan, Ummul Husayn, Ummul Muhsin, Ummul Imam, Umme Abiha da Ummul Mu’uminina kuma an kawo wadannan mukamai a cikin sallamar da ake yi mata.
Haka nan ya zo a cikin al-Manaqib cewa a cikin Sama an san ta da sunan al-Nuriyyah (mai haskakawa), al-Samawiyyah, da al-Haniya. Sunanta al-Haniyah saboda tana da kirki da son mijinta da 'ya'yanta.
Kuyi like akan wannan post sannan Kuyi share domin 'yan uwa su amfana. Idan da wani gyara ko Korafi to kuyishi a comment.
KUYI FOLLOWING DIN MU A
Website din mu
👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Facebook page din mu:
👇👇👇👇👇👇👇👇👇