RANAR HAIHUWAR MANZON ALLAH (SAWW) DA KUMA ABUBUWAN BAN MAMAKI DA SUKA FARU





RANAR HAIHUWAR MANZON ALLAH (SAWW) DA KUMA ABUBUWAN BAN MAMAKI DA SUKA FARU


Kamar yadda kuka sani cewa Malaman Imamiyyah Sun cinma Matsaya akan cewa an haifi Manzon Allah (Saww) Ranar 17 ga watan Rabi'ul Awwal, Wasu kuma suna ganin 12 ga Watan Rabi'ul Awwal, Wasu kuma suna tunanin 8 ko 10 ga Watan Rabi'ul Awwal ne. Kadan daga cikinsu na ganin cikin Watan Ramadan ne. 

Kuma an Haifi Manzon Allah (S) Ranar Juma'a, a lokacin da Rana take Faduwa, a shekarar Giwaye. 

A wata ruwayar lokacin da rana take fitowa. Kuma an Haifi Manzon Allah a Garin Makkah a Gidan Muhammad bn Yusuf. Wanda daga baya khizran Mahaifiyar Haruna Rashid Ta Maida Wannan Daki Zuwa Masallaci. 

Marubucin Littafin Adade Qawiyyah Yace “Haihuwar Manzon Allah ta Kasance bayan kwanaki 55 ko kuma 45 ko kuma kwana 30 bayan  Hallakar da Mayakan Giwaye a Ranar Juma'a 17 ga Watan Rabi'ul Awwal  lokacin da Rana take Faduwa”. 

An Naqalto daga Abu Talib Yace “wani Dare ina Barci a Hajare Ismail Sai nayi Wani Mafarki mai ban Mamaki Sai Wani Boka Ya ganni ina ta kyarma sai ya kalleni cikin natsuwa sai Ya Tambaye ni Yace ya kai Shugaban Larabawa miya Sameka Sai nace dashi ”yau da nake barci a Hajare Ismail nagani a cikin barci wata bishiya tana girma a bayana kuma tayi girma sosai har ta Shiga Sararin Samaniya, Sannan kuma reshenta Ya Barbazu Gabas da Yamma Sai Wani Haske Ya Fashe Wanda Wannan haske ya ninka Hasken Rana Sau 70 Larabawa da wadanda ba larabawa ba sun duka Gaban Wannan Bishiya, Shi kuma haskenta da Tsawonta Sai Qaruwa Yakeyi. Sai ga wani gungu na Quraishawa sunzo domin sare Wannan Bishiya, a lokacin da suka kusance ta,Sai ga wani Saurayi kyakkyawa da kyakkyawar Shiga ya kamasu ya karya masu Baya da kuma Idanunsu. Sai na mika Hannu domin in Ciri reshe daga gareta, Sai Wannan Saurayi yayi kuka Yace Baka da Rabo a cikin ta sai nace mashi Wannan fa Bishiyata ce ya kace bani da Rabo a cikinta Sai ya bani Amsa da cewa Wdanda suke da rabo da ita sune wadanda suka nemi dawwama da Ita. Sai na farka cikin tsoro na abinda na gani”. 

A lokacin da Wannan Boka yaji abinda na gaya mashi sai fuskarsa ta canza, yace idan har Gaskiya ka fadi to za'a haifi yaro daga  tsatsonku wanda zai Mallaki Gabas da Yamma kuma zai zama annabi. 
Bayan haka sai Abdulmutallib yace ma Abu Talib Kayi Qoqari ka zama Wannan Saurayi Wanda ke taimakon shi. Abu Talib ya Kasance yana cewa lalle Wannan Bishiyar Abul Qasim ne. 
Ibn Shahr Ashob ya ruwaito cewa lokacin Da Mamun yaje domin sanin ilimin Taurarin Hakim Eezadkah ya tambayi masanin Taurarin cewa duk da Wannan Ilimi da kuke dashi miyasa ba kuyi Imani da Manzon Allah ba sai ya bashi amsa da cewa tayaya zaniyi imani dashi alokacinda aka haife shi a wani yanayin da ba'a Taba Haihuwar Wani Annabi ba. An Haife shi a Tauraron Mushtari (Jupiter) da kuma Utarud(Marcury) da kuma Zuhar (Venus) da kuma Mireekh(Mars) Juma duk Wanda Aka haifa a wadannan Taurari dole ne ya mutu nan take, amma idan ya rayu zaya mutu cikin  kwana 7 amma shi (Manzon Allah S) amma shi an haife shi a Wannan yanayi amma ya rayu Shekara 63,Wannan yana daga cikin Mu'ujizarshi. 

A taqaice Mushtari (Jupiter) alama ce ta Ilimi, Hikima, Hankali da sauransu
Ita kuma Utarud (Marcury)  alama ce Ladabi, fara'a, Balaga(iya magana) da kuma Tasiri
Ita kuma Zuhar (Venus) alama ce ta kyau, ni'ima, janhankali da Kamshi
Ita kuma Mireekh (Mars) alama ce ta Sahada, Karfi da Nasara. Sai Allah (T) ya hada duk wadannan darajojiga Manzon shi (S A W W). 

Zamu Cigaba Insha Allah... 

Post a Comment

Previous Post Next Post