Kafofin watsa labarai sun ba da rahoton cewa, an harba rokoki da dama daga kasar Lebanon zuwa wani matsugunin Isra’ila da ke Al-Jalil a arewacin Falasdinu da ta mamaye.
Tashar talabijin Channel 12 ta kasar Isra'ila ta bayar da rahoton cewa a yau Juma'a an harba rokoki da dama daga kasar Lebanon zuwa yankunan da Isra'ila ta mamaye a Al-Jalil da ke arewacin kasar Falasdinu.
Har ila yau, kungiyar Islamic Resistance a Iraki, gamayyar mayakan da ke yaki da ta'addanci, ta bayyana a ranar Juma'ar da ta gabata cewa, sun kai hari kan sansanin jiragen sama na Ovda, da ke kudancin yankunan da aka mamaye, mai tazarar kilomita 40 daga arewacin birnin Eilat mai tashar jiragen ruwa.
Kungiyar gwagwarmayar Islama ta Iraki ta ce dakarunta sun kai hari kan rundunar sojojin sama ta Isra'ila da ke sansanin "Ovda Airbase", ta hanyar amfani da jirage marasa matuka, a matsayin wani aiki na hadin gwiwa da Gaza a cikin yakin kisan kare dangi da Isra'ila keyi.
A 'yan sa'o'i kadan da suka gabata ne mayakan Islama na kasar Iraki suka sanar da kai wani hari da jiragen yaki marasa matuka kan sansanin Elifelet na gwamnatin yahudawan sahyoniya a kasar Palasdinu da ta mamaye.
Allah ya qara taimakon 'yan gwagwarmaya Musulunci a duk inda suke, ya kuma kawo mana qarshen Isra'ila da Mataimakan ta.
