Hezbollah a Shirye Take Don Yaƙi da Gwamnatin Isra'ila


IRNA ta Ruwaito cewa Shugaban Majalisar zartarwar kungiyar Hizbullah Hashim Safi Al Din ya bayyana cewa Kungiyar gwagwarmaya ta kasar Labanon a shirye take da ta dauki dukkan matakan da suka dace domin tunkarar irin ta’asar da gwamnatin sahyoniyawan Isra’ila ke yi.

Safi Al Din ya soki shirun da al'ummomin duniya suke yi kan kisan Kiyashin da akeyi a Gaza, kamar yadda kafafen yada labarai na Larabawa suka ruwaito.

Kungiyar Hizbullah ta mallaki makamai ne ba don komai ba, face dai don kare al'ummarta da kuma taimakon al'ummar da ake zalunta a wannan yanki, in ji shi.

Abinda fararen hula na Gaza ke fama da shi a cikin watanni bakwai da suka gabata ba a taba ganin irinsa ba, in ji jami'in.

Ya ci gaba da cewa mun tsaya tsayin daka da wanda ake zalunta sannan kuma muna adawa da azzalumi tun lokacin da aka fara yakin kisan kare dangin.

Akalla mutane 34,049 yawancinsu mata da yara ne aka kashe a munanan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza tun fara yakin.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post