Manjo-Janar Aharon Haliva, shugaban hukumar leken asirin sojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayyana.
Ana dai danganta murabus din ne da kasa dakatar da harin ba zata da kungiyar Hamas ta kai wa yankunan da ta mamaye a ranar 7 ga watan Oktoba a daidai lokacin da ake ci gaba da takun saka tsakanin Haramtacciyar Kasar Isra'ila da Iran.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta fitar ta ce: Shugaban sashen leken asiri, Manjo Janar Aharon Haliva tare da hadin gwiwar babban hafsan hafsoshin sojin ya bukaci kawo karshen mukaminsa biyo bayan alhakin da ya ke da shi na shugaban hukumar tsaron kasar a cikin lamuran da suka faru. Oktoba 7."
Ba da daɗewa ba bayan harin na 7 ga Oktoba, an ba da rahoton Haliva yana cewa: "Tun daga wannan safiyar na fahimci cewa ya komai ya ƙare."
Da dama dai na ganin cewa murabus din nasa na da alaka da rikicin baya-bayan nan da Iran, saboda rashin kididdigar da ya yi na martanin da Teheran ta mayar kan harin da aka kai mata akan ginin ofishin jakadancinta da ke Damascus, wanda ya yi sanadin harba makamai masu linzami kan yankunan da Isra'ila ta mamaye a makon jiya.
