Mazaunan Isra'ila sun kashe Falasdinawa biyu a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, a cewar jami'ai da shaidun Falasdinawa na gani da ido, bayan da aka shafe mako guda ana tashe tashen hankula a yankin.
kamfanin dillancin labaran WAFA ya labarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ma’aikatar lafiya ta Falasdinu cewa, an gano mutanen da harin ya rutsa da su a kusa da kauyen Aqrabah da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan, mai nisan kilomita goma sha takwas (mil 11.18) kudu maso gabashin Nablus.
Salah Bani Jaber, magajin garin Aqrabah, wanda ya ganewa idanunsa harin da ‘yan Mazaunan suka kai, ya ce wasu mazaunan su kusan 50 ne, da dama daga cikinsu dauke da makamai, suka kai wa ‘yan unguwarsu hari.
Magajin garin ya ce "sun far wa mazauna garin tare da yin harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da ya kai ga mutuwar 'yan kasar biyu," in ji magajin garin, ya kara da cewa "har yanzu sojojin mamayar suna rike da gawarwakin."
"Akwai sojojin Isra'ila a wurin da suke tsaye suna kallon mazauna," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce sojojin Isra'ila sun hana motocin daukar marasa lafiya zuwa yankin da kuma kula da wadanda suka jikkata.
A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce tana duba lamarin.
Falasdinawa da ke zaune a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye na fuskantar barazana a kodayaushe yayin da Isra'ilawa 'yan kawanya dauke da makamai ke ci gaba da kai munanan hare-hare a kan su, da iyalansu, da gidajensu domin daukar fansa.
Jami'an ma'aikatar lafiya ta Falasdinu sun bayar da rahoton a ranar Litinin cewa, an kashe Falasdinawa hudu a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa mazauna yankin tun ranar Juma'a.
Hare-haren na baya-bayan nan wani bangare ne na tashe-tashen hankula da ke kara ta'azzara tun bayan kazamin yakin da Isra'ila ta yi a Gaza. Yakin ya kashe akalla mutane 33,797 a Gaza, akasari mata da kananan yara, ya kuma raunata wasu mutane 76,465, a cewar ma'aikatar lafiya a yankin.
Mazauna masu dauke da makamai da sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa 460 tare da raunata wasu 4,800 a yammacin gabar kogin Jordan da suka mamaye tun ranar 7 ga watan Oktoba.
A ranar 13 ga watan Afrilu, 'yan Isra'ila mazauna yankin sun jagoranci wani gagarumin hari a kauyen al-Mughayyir, inda suka kashe Bafalasdine guda tare da jikkata wasu 25 na daban.
Tun daga wannan lokacin, mazauna garin suka fara kai hare-hare a wasu garuruwa da kauyukan da ke kusa da Ramallah, ciki har da Bukra, Dayr Dibwan da kuma Kfar Malik.
Rikicin matsugunan da ake yi wa Falasdinawa da dukiyoyinsu ya zama ruwan dare a Yammacin Gabar Kogin Jordan, kuma ba kasafai mahukuntan Isra'ila ke tuhumar su ba.
Ta'addancin ya hada da kona kadarori da kona masallatai, jifa da duwatsu, da tumbuke amfanin gona da itatuwan zaitun, da kai hare-hare kan iyalai masu rauni da dai sauransu.

