Yadda Hauzah ta Karrama Sheikh Zakzaky a Matsayin Abin Koyi Gurin Isarda Sakon Musulunci



Shugaban makarantar hauza na Iran ya ce, dukkan ma'abota girman kan duniya suna qalubalantar Gwagwarmayar Marigayi Imam Khumaini da juyin juya halin Musulunci, amma wannan Gwagwarmayar bata qare ba, saboda irin su Shaikh Zakzaky da Mujahidan da ake alfahari da su a duniya sun bi Imam Khumaini, gurin jagoranci, juyin juya halin Musulunci don son Musulunci, adalci, 'yanci da ruhiyya. "

Shugaban makarantar hauza ta Iran Ayatullah Alireza Arafi ya bayyana a wajen taron karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, wanda cibiyar kula da makarantun Islama da ke birnin Qum tare da hadin guiwar Jami’ar Al-Mustafa dake birnin Qum,” Marigayi Imam Khumaini (RA) ya daga muryar Musulunci da ‘yanci.

Yayin da yake mai nuni da cewa wannan shine karo na 60 da fara tuna wannan lamari, in ji shi, “a bisa iko na Ubangiji, an samu sabon yunkuri a Afirka.”

Shugaban makarantar hauza na Iran ya bayyana cewa, magabatan harkar Musulunci sun daga tutocin juyin juya halin Musulunci a kasashen Palastinu, Labanon, Yemen da Afirka bayan rabin karni inda ya ce: Muna bikin cika shekaru 60 da juyin juya halin Musulunci, wanda ya kasance. Imam Khumaini (RA) ne ya assasa shi.”

Da yake mai nuni da cewa sama da rabin karni mun wuce wahalhalu da dama, kuma mun juyo da matsaloli dubbai, ya ce“duk da malamai da ma’abota girman kai sun yi adawa da Gwagwarmayar marigayi Imam Khumaini da juyin juya halin Musulunci, amma wannan gwagwarmayar ba a rufe bakinta ba, domin irin su Shaikh Zakzaky da Mujahidai na duniya, da suka hadu da Imam (RA) da juyin juya halin Musulunci don son Musulunci, Adalci, 'yanci da ruhiyya. .”

Ayatullah Arafi ya yi nuni da cewa makiya suna da daruruwan munanan makirce-makircen kuma ya fayyace cewa, “Daya daga cikin irin wadannan makircin shi ne kafa kungiyoyin ta’addanci irinsu ISIS”.

Ya bayyana cewa juyin juya halin Musulunci yana gayyatar bil'adama da ake zalunta da su tashi tsaye wajen yakar azzalumi, ya kuma ce: Abinda juyin juya halin Musulunci yakeso shine gabatar da Musulunci ga duniya.

Ayatullah Arafi ya yi nuni da cewa a ko da yaushe juyin juya halin Musulunci yana jaddada mutunta malamai da manyan mutane da kuma al'ummar sauran kasashe, yana mai cewa: A makarantun hauza muna kokarin gabatar da addini ga sauran mutane.

Shugaban makarantun hauza na Iran ya kara da cewa: Mun kulla yarjejeniya da shahidan gwagwarmaya cewa za mu ci gaba da tafiya tare da jagororin Musulunci a duk fadin duniya.

Ya kuma jaddada cewa, sakon wannan taro shi ne girmama janar-janar da sojojin wannan tafarki mai tsarki da kuma bayyana hadin kai da malamai a duk fadin duniya.

Ayatullah Arafi ya yi nuni da cewa, muna sa ran gwamnatocin kasashen Afirka za su koma ga gwamnatocinsu na asali da kuma Musulunci, Ayatullah Arafi ya ce: "Wannan shi ne batun juyin juya halin Musulunci da makarantar hauza, kuma muna son daukaka da 'yancin ku."

Post a Comment

Previous Post Next Post