Wadannan Jerin Sallolin Masu Zuwa Anason yinsu a kowane Dare na Watan Rajab
A. A kowane dare ana so a yi Sallah mai raka'a biyu, wanda a kowace raka'a ake karanta suratul Fatiha sau daya da kuma suratul kafirun sau uku (x3) sai kuma Suratul Tauhid sau daya (x1).
Bayan an idar da sallar sai a daga hannaye zuwa sama sannan a karanta:
لاَ إِلٰهَ إِلاَّ ٱللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ لَهُ ٱلْمُلْكُ وَلَهُ ٱلْحَمْد يُحْيِي وَيُمِيتُ وَهُوَ حَيٌّ لاَ يَمُوتُ بِيَدِهِ ٱلْخَيْرُ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ وَإِلَيْهِ ٱلْمَصِيرُ وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِٱللَّهِ ٱلْعَلِيِّ ٱلْعَظِيمِ اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ ٱلنَّبِيِّ ٱلْأُمِّيِّ وَآلِهِ
An ruwaito Manzon Allah (saww) ya ce, idan mutum yayi wannan Sallar ya kuma karanta wannan addu’ar, Allah Ta’ala zai biya masa buqatunsa, kuma zai ba shi ladan Hajji sittin da ‘ Umrah.
Sauran Salloli a Watan Rajab
B.) Haka nan kuma an ruwaito Manzon Allah (saww) yana cewa Allah Madaukakin Sarki zai gafarta wa duk wanda yayi salloli raka'a goma, a dare daya a watan Rajab, yana karanta suratul Fatiha sau daya (x1), sannan kuma ya maimaita suratu al-Tauhid sau uku (x3).
C) Manzon Allah (s.a.w.w) ya ce: "Wanda ya karanta Suratul Ikhlass sau 100 (50 X 2) a cikin raka'a 2 na sallah a cikin dare daya na watan rajab, zai zama kamar wanda ya yi azumin shekara 100.... .: Ref Mafatih].
D) Manzon Allah (s.a.w.w) ya ce: “Allah zai gafarta wa duk wanda yayi sallah raka’a goma, a dare daya a watan Rajab, yana karantawa a kowace raka’a; Suratul Fatiha sau daya (x1) +Suratul Kaferoon sau daya (x1) +Suratul Tauhidi sau uku (x3).” [Reference: Mafatih].
Tags
Watan Rajab
