*YAA MAHDI *
*Hura wuta a qofar gidan Zahra (SA)*
Lokacin da Imam Ali ya ga rashin amincewa na mutane sai ya gane cewa suna neman uzuri ne don kada su taimake shi, kuma suna taruwa a wajen khalifa, sai ya zauna a gidansa bai fito ba. Sai wane ya ce wa Khalifa, ‘Me ya sa ba ka aika da sako ga Ali ya zo ya yi mubaya’a a hannunka ba? Kowa ya yi mubaya’a sai shi da mutum hudu.
Shi Wane (wanda akeba shawara) ya kasance mai taushin zuciya kuma matsakaiciya kuma mai taka tsantsan a cikin al'amura yayin da wane (Mai bada shawara) ya kasance zuciyarsa kamar dutse da kaushi, kuma ya mallaki harshe mai kaifi don haka sai Wane (Mai bada shawara) ya ce: "Zan aika Qunfudh ya nemi Ali, domin Qunfudh zuciyarshi kamar dutse take, mai zafin rai da rashin tausayi, bawa ne ‘yantacce amma daga zuriyar Adi b. Ka’ab.”
Sai Wane (wanda aka ba Shawara) ya aika Qunfudh tare da wasu zuwa ga Ali, a lokacin da Qunfudh ya zo gidan Ali, ya fara neman izinin shiga, amma Imam ya ki bashi umurni. Sahabban Qunfudh suka komo wurin wane da wane wadanda suke zaune a masallaci tare da gungun mutane suka ce Ali bai ba su izinin shiga gidansa ba. Jin haka sai wane (wanda ya kawo shawarar) ya ce: ‘Ku koma gidan Ali, idan kuma bai yi muku izini ba, to ku shiga ba da izini ba.
Suka zo kofar gidan Imam Ali, suka nemi izinin shiga. Sayyidah Fatimah ta zo kofar gida ta ce, ‘Na hana ku shiga gidana ba tare da izini ba.
Qunfudh ya zauna a gidan yayin da sahabban Qunfudh suka sake zuwa wurin wane da wane suka ba su labarin kin amincewar Fatima (SA).
Jin haka sai Wane (Wanda ya bada shawara) ya fusata ya ce, ‘Me ya hada mu da ayyukan mata! Sai wannan wane (wanda yabada shawara) yabada umurni a tattara itace sai suka nufo kofar gidan Fatimah. Suka watsar da itacen a kofar gidan yayin da ‘Ali da Fatimah da Hasan da Husaini suke cikin gidan. Sai wane (wanda ya bada shawara) ya ce, ‘Na rantse da Allah! Idan ba ka fitoba ya Ali ka yi mubaya’a a hannun halifan Manzon Allah ba, zan kona ka.” Ali da Fatima suka ji bukatarsa, sai Fatima ta amsa masa da cewa, ‘Me ya sa kukeyi mana haka?'
Sai wane (wanda yabada shawara) ya ce: “Bude kofa ko in kona ku!
Fatima (As) ta ce, ‘Ba ku ji tsoron Allah ba har yanzu, kuma har yanzu kuna son shiga gidana?
Wane bai tafi ba, sai ya ce wa abokansa su kawo wuta a nan ne ya kona kofar gidan Fatimah, kuma ya tura kofar da karfi, sannan ya shiga ciki. Ganin haka sai Fatima ta tsaya a gabansa ta yi kira, ‘Ya baba! Ya Manzon Allah!’
‘Sai wane ya zare takobinsa ya bugi Fatima a gefenta, sai ta yi kira, ‘Ya baba!
Sai Wane ya daga bulala ya bugi hannun Fatimah, sai ta fashe da kuka tana cewa, ‘Ya Manzon Allah! Kana ganin irin munin da Wane da Wane suka yi mana!
A nan ne Imam Ali ya yi tsalle ya kama kwalar wane ya jefar da shi kasa da karfi har wuyansa da idonsa suka ji rauni. Sai ya yi niyyar kashe shi, amma kwatsam ya tuna Alqawarin Annabi (ta yayi haquri) sai yayi kira, ‘Ya dan wane (Imam ya kira sunane)! Na rantse da Allah wanda ya daukaka Muhammad zuwa ga darajar Annabci da cewa da ba a hukunta umarnin Allah ba, kuma Manzon Allah bai yi mini wa'adin (hakuri) ba, da kun gane wahalar shiga gidana!'
Sai Wane (wanda Imam yaja ma kunne) ya aika wani mutum wurin Wane yana neman taimakonsa, sai ga wata tawagar magoya bayan Wane suka zo suka shiga gidan Imam Ali.
Ganin haka sai Imam Ali ya tashi ya zare takobinsa. Qunfudh ya gudu ya koma wurin Wane (wanda ya turo qarin mataimaka) domin yana tsoron kada Imam Ali ya yake su da takobinsa, domin ya san Gwarzantaka da jaruntar Imam Ali a cikin yake-yake.
Wane (wanda ya turo qarin mataima ka) ya ce wa Qunfudh, “Koma gidan Ali Idan ya fito daga gidansa, ku kawo mini shi, ko kuwa ku ƙone gidan da mazaunansa!’
Qunfudh ya koma ya shiga gidan Ali tare da abokansa ba tare da ya nemi izini ba, sai Ali ya yi kokarin ya dauke takobinsa, amma Qunfudh ya riga shi ya kwace takobi daga gare shi. A lokacin ne Fatima ta shiga tsakani domin ta kare Imam Ali, sai Qunfudh ya dauki bulalarsa ya buga mata (la'anar Allah ta tabbata a gare shi da sahabbansa, kuma Allah ya jefa shi cikin ramin jahannama a lahira). Lokacin da ta rasu (Fatimah) anga alamar ( bulala) a hannunta kamar na abin hannu.
Daga nan sai aka kawo Imam Ali da karfi wajen Wane (Wanda ya tura qunfudh), yayin da Wane (wanda Imam yajama Kunne a gidansa) yake tsaye a kansa da takobin a zare, da sauran su, wato Khalid b. al-Walid, Abu ‘Ubaydah al-Jarrah, Salim ‘yantaccen bawan Abu Huzaifa, Ma’adh b. Jabal, al-Mughirah b. Shu'bah, Usayd b. Huzair, Bashir b. Sa’ad da sauran su na tsaye a wajen Wane cikin kayan yaki.
Kukan Fatimah da hukuncinta na Addu'a akan maharan*
Al-Ayyashi yana cewa: “(Bayan an kai Imam Ali wajen Halifa), sai Fatima ta fito (daga gidanta ta tafi Masallaci) ta juya wajen Halifa ta ce, “Shin kana nufin ka tafi da mijina daga gareni, ka maidani bazawara? Idan ba ku sake shi ba, na rantse da Allah, zan wargaza gashina in yaga kwalata (wuyan riga), sannan in tafi kabarin mahaifina, in roki Allah a kanku.
Nan take Fatima ta kama hannun Hasan da Husaini ta nufi kabarin Annabi. Imam Ali yana sane da abin da zai biyo baya ( zata yi Addu'a akan wadannan mutanen) sai ya ce wa Salmanu, ‘Ka je ka hana Fatima ‘yar Muhammadu (S) ! Kamar na ga bangarorin Madina biyu suna girgizawa, sannan kuma kasa ta hadiye su. Wallahi! Idan Fatima ta wargaza gashinta ta yaga kwalar tufarta yayin da take tafiya qabarin Manzon Allah (Saww) kuma ta roki Allah, mutanen Madina ba za su samu jinkiri ba, sai kasa ta hade su baki daya!
Salman ya yi gaggawar isa wurin Fatimah, ya ce mata, Ya ‘yar Muhammadu (Saww)! Allah ya sanya Babanki rahama ga talikai! Don Allah ki koma Gidanki kada ku yi Addu'a.'
Fatimah ta ce: ‘Ya Salmanu! Suna burin kashe Ali, kuma hakurina ya ragu, bari in tafi kabarin mahaifina don in wargaje gashina, in yayyage kwalawar tufana, in kai qara ga Allah.
Salmanu ya ce, ‘Ina tsoron Madina ta girgiza (saboda addu’o’in ki) kasa ta hadiye kowa. ‘Ali da kansa ya aiko ni gare ki da cewa ki koma gidanki, in kuma roke ki da ki daina yin addu'a.
Jin haka sai Fatima ta ce, ‘In haka ne zan koma, Zani jure, in yi masa biyayya.
Allamah al-Tabarsi ya ruwaito a cikin littafinsa al-Ihtijaj cewa Imam Ja'afar as-Sadik ya ce a lokacin da aka fito da Imam Ali daga gidansa, sai dukkan matan Bani Hashim suka fito daga gidajensu, suka yanke shawarar tafiya zuwa kabarin manzon Allah. Fatima ta yi kira, ‘Ku bar dan uwana! Na rantse da Allah wanda ya zabe Muhammadu (Saww) da gaskiya! Idan ba ku sake shi ba, zan wargage gashina, in dora rigar Annabi a kaina, in yi tawassuli a wurin Allah, kuma rakumin Annabi Salihu baifi soyuwa a wurin Allah fiye da ‘ya’yana ba.’
Zamu cigaba Insha Allah....
Allah Madaukakin Sarki kaba Jagora Lafiya, Katsareshi daga Sharrin Maqiya Ka kare mana Imanin Mu, Ka bamu juriya da Sabati a Addinin nan kuma ya Rabbi kasa damu Za'ayi.
Idan da wani gyara ko shawara to Kuyi shi a comment, sannan Kuyi like akan wannan post sannan Kuyi share domin 'yan uwa su amfana.
*KUYI FOLLOWING DIN MU A*
-Website din mu
👇👇👇👇👇👇👇👇👇
www.yaa-mahdi.blogspot.com
- Facebook page din mu
👇👇👇👇👇👇👇👇👇
https://free.facebook.com/Yaa-Mahdi-104755022030542