AYYUKAN DAREN JUMA’A
Daren Juma'a, ana so a karanta surori (Surah) na Alkur'ani mai girma:
(1) Suratul Isra ’(Bani Isra’il; No. 17),
(2) Suratul Kahf (No. 18),
(3) Ka Karanta Wadannan Surori guda Uku Masu Zuwa Zaka fara Karanta Ya-Sin, Sannan Sai Suratul Shu’ara ’(Na 26), Suratul Naml (Na 27), da Suratul Qasas (Na 28),
(4) Suratul Sajdah (Na 32),
(5) Suratu Yasin (No. 36),
(6) SurahSad (No. 38),
(7) Suratul Ahqaf (Na 46),
(8) Suratul Waqiah (No. 56),
(9) Suratu Fussilat (No. 41),
(10) Suratul Dukhan (Na 44),
(11) Suratul Tur (Na 52),
(12) Suratul Qamar (Na 54), da
(13) Suratul Jumu’ah (Na 62).
Idan babu isasshen lokacin karanta duk waɗannan surorin, mutum na iya zaɓa daga Suratul Waqiah Zuwa Qarshe.
An ruwaito Imam Sadik (a.s) yana cewa wanda ya karanta suratul Isra'i kowane daren Juma’a zai shiga cikin Sahabban Imam Mahdi (a.s).
An kuma ruwaito shi (a.s.) yana cewa wanda ya karanta suratul Kahfi a daren Juma'a zai mutu a matsayin shahidi kuma za a tashe shi cikin layin shahidai (a ranar tashin kiyama).
An ruwaito shi (as) yana cewa duk wanda ya karanta surori guda uku da suka fara da Ya-Sin a daren Juma'a za a hada shi da manyan waliyyan Allah Madaukakin Sarki, Kuma Za'a sashi cikin kariyarsa, ba zai taba shiga wahala ba a rayuwarsa ta duniya, kuma za a ba shi fiye da jin daɗinsa a Ranar Kiyama.
An ruwaito shi (as) yana cewa duk wanda ya karanta suratul Sajdah a daren Juma'a za a ba shi Littafin Ayyukansa a hannunsa na dama, ba za a yi masa tambayoyi game da miyagun ayyukansa ba, kuma za a hada shi da sahabban Muhammadu da Iyalan gidansa - aminci ya tabbata a gare su baki daya.
An ruwaito Imam Muhammad al-Baqir (as) ya ce wanda ya karanta Suratus Sad a daren Juma'a za a ba shi jindadin duniya da na Lahira ta kyakkyawar hanya da babu wanda zai cancanci sai Annabawa da Mala'iku da za a ba shi izinin shiga Aljanna da duk wanda yake so a cikin gidansa har da bayi.
An ruwaito Imam Ja’afar Sadik (as) ya ce wanda ya Karanta a ranar Juma’a ko daren Juma’a suratul Ahqaf zai tsira, da Allah Madaukakin Sarki, daga ta’addanci a rayuwar duniya kuma zai samu tsira daga firgici na Ranar Kiyama.
An ruwaito shi (as) yana cewa duk wanda ya karanta suratul Waqiah a daren Juma'a Allah Madaukakin Sarki zai so shi, dukkan mutane za su so shi, za su kubuta daga dukkan kunci, talauci, da masifu a cikin wannan rayuwar duniya, kuma zaya kasance tare da sahabban Imam Ali Ameer al-Momineen (as) saboda an ba shi wannan surar.
An kuma ruwaito cewa Wanda ya karanta Suratul Jumu’ah a daren Juma’a an yanke hukuncin kaffara (gafarta zunubai) ga munanan ayyukan da aka aikata cikin mako. An ruwaito irin wannan falalar don karanta suratul Kahfi a daren Juma'a ko bayan Sallar Asubahi da farilla biyu na Juma'a.