Ƙungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta Yemen ta bayyana cewa za ta dakatar da ayyukan da take yi a Tekun Bahar Maliya domin goyon bayan mutanen Palasɗinu idan aka fara aiwatar da tsagaita wuta a Gaza ranar Lahadi.
Kakakin Ansarullah, Mohammed al-Bukhaiti, ya bayyana a ranar Asabar cewa ƙungiyar ta Yemen tana goyon bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Hamas da Isra’ila.
“Idan Isra’ila ta dakatar da hare-haren da take kaiwa a Gaza … [za mu] dakatar da ayyuka, ciki har da hare-hare kan jiragen ruwa na soji da na kasuwanci,” in ji al-Bukhaiti.
Shugaban dakarun Ansarullah, Abdel Salam Al-Houthi, shima ya yaba da yarjejeniyar tsagaita wutar, yana mai bayyana ta a matsayin cigaban da ya dace.
“An tilastawa Abokan gaba na Isra’ila da Amurka zuwa wannan yarjejeniya bayan watanni na aikata manyan laifuka,” in ji shi.
Ya jaddada cewa matsayar siyasar Hamas tana nan daram wajen nuna goyon baya ga jajircewa da sadaukarwar da mutane da ’yan gwagwarmaya suka yi a filin daga da sauran wurare.
“Jaruman Mujahidai da sadaukarwar ’yan uwa a Zirin Gaza abin ban mamaki ne, abin alfahari, kuma suna raunana kwarin gwiwar abokan gaba.”
A lokaci guda, Ansarullah ta yi gargaɗi ga “mayaƙan gaba” a Tekun Bahar Maliya kan “sakamakon” duk wani hari da za a kai wa Yemen yayin tsagaita wuta a Gaza.
A cikin wata sanarwa da ta fitar safiyar Lahadi, ƙungiyar ta ce, “Za mu mayar da martani kan duk wani hari da ayyukan soja na musamman ba tare da iyaka ko ƙayyadewa ba.”
“Dakarun sojin Yemen sun fara hare-haren soja kan Isra’ila a watan Nuwamba 2023, domin mayar da martani ga kisan kiyashin da aka yi a Gaza, inda aka kashe kimanin Falasɗinawa 47,000 zuwa yanzu.”
A cikin ayyukanta, Yemen ta kai hari kan jiragen ruwa da ke da alaƙa ko mallakar Isra’ila a Tekun Bahar Maliya waɗanda ke kan hanyarsu zuwa tashoshin jiragen ruwa a yankunan da aka mamaye.
Wadannan hare-haren sun yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin Isra’ila.
Amurka, Birtaniya, da Isra’ila sun kaddamar da daruruwan hare-hare a Yemen don hana ƙasar ci gaba da ayyukan sojinta na goyon bayan Palasɗinu.
Duk da haka, Yemen ta ci gaba da nuna jajircewa wajen goyon bayan gwagwarmayar ƙin zalunci, tana mai alƙawarin ci gaba da hare-harenta har sai Isra’ila ta kawo ƙarshen farmakin da take kaiwa a Gaza.
Bayan watanni 15 na kisan kiyashi a Gaza, Isra’ila ta kasance tilas ta amince da tsagaita wuta tare da karɓar sharuɗɗan tattaunawar Hamas, bayan da ta kasa cimma burin yaƙinta, ciki har da “ƙwace Hamas baki ɗaya.”