Sojojin Isra'ila sun harbe matashi Bafalasdine har lahira a Tel Aviv, wanda ke cikin yankunan da Isra'ila ta mamaye, bisa zargin kai hari da wuka.
A cikin wata sanarwa, 'yan sandan Isra'ila sun yi ikirarin cewa matashin Falasdinawan ya kai wa wani mutum hari da wuka a kan titin Levontin ranar Asabar da rana, inda ya ji masa rauni mai tsanani, kafin wani dan yankin da ke dauke da makami ya harbe shi har lahira a wurin.
Wanda aka ji wa rauni, wani mutum mai shekaru 30, an garzaya da shi zuwa asibitin Ichilov a mawuyacin hali. Daga bisani, asibitin ya bayyana cewa halin nasa ya inganta, kuma baya cikin hatsarin rayuwa.
Kan TV News, gidan talabijin na jama’a a Isra’ila, ya bayyana sunan matashin Falasdinawan da aka kashe da Salah Yahya, mai shekaru 19, daga birnin Tulkarm da ke arewacin yankin Yammacin Kogin Jordan.
'Yan sandan sun bayyana cewa suna bincike kan yadda lamarin ya faru.
Zargin kai harin da wuka ya faru ne awanni kafin yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta fara aiki.
An tilastawa Gwamnatin Isra’ila amincewa da yarjejeniyar tsagaita wutar, inda ta karbi sharuɗɗan tattaunawar Hamas na dogon lokaci.
Tsagaita wutar da aka dade ana jira na dauke da wani mataki na farko mai tsawon kwanaki 42, wanda zai dakatar da yakin kisan kare dangi da Isra’ila ta shafe fiye da watanni 15 tana yi a Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan Falasdinawa 47,000.
A matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar, za a sako mutane 33 da ake garkuwa da su a Isra'ila daga Gaza da aka killace, a madadin sakin fursunonin Falasdinawa 735 da kuma wasu 1,167 daga Gaza.
A cewar Mahmoud Basal, mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta Falasdinawa, akalla Falasdinawa 122, ciki har da yara 33 da mata 33, sun rasa rayukansu yayin da wasu fiye da 270 suka jikkata sakamakon hare-haren sama da Isra’ila ta kai a Gaza bayan sanarwar tsagaita bude wuta.
A ranar 7 ga Oktoba, 2023, Isra'ila, tare da goyon bayan Amurka da kawancenta na yammacin duniya, ta fara yakin Gaza domin mayar da martani ga farmakin "Dufanul Al-Aqsa" na kungiyar Hamas, wanda ya yi nufin kalubalantar yakin danniya da Isra’ila ta shafe shekaru tana yi kan Falasdinawa.
A ranar 21 ga Nuwamba bara, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta fitar da takardun kama firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan harkokin tsaro Yoav Gallant kan laifukan yaki da laifuka kan bil’adama a Gaza.