Kakakin rundunar, Birgediya Janar Yahya Saree, ya bayyana hakan ranar Asabar, bayan Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi ikirarin cewa Tel Aviv na da “hakki” na ci gaba da yakin kisan kare dangi da ta kwashe watanni 15 tana kaiwa Gaza, duk lokacin da ta ga dama.
Netanyahu ya kara da cewa gwamnatin Isra'ila na iya ci gaba da kai hare-haren soji duk da yiwuwar aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin gwamnatin Isra’ila da kungiyoyin gwagwarmaya na Gaza.
“Kakakin ya ce rundunar makamai masu linzami ta dakarun Yaman ta kai hare-hare biyu kan wasu muhimman wurare guda biyu da ke karkashin ikon maƙiya Isra’ila a yankin Umm Al-Rashrash, da ke kudancin Palasdinawa da aka mamaye,” in ji Saree. Wannan wurin yana nuni da tashar jiragen ruwa ta Eilat da sauran wuraren da ke kusa da ita a kudancin yankunan da aka mamaye.
“Harin farko an kai shi ta amfani da makami mai linzami samfurin Thulfiqar,” in ji kakakin, yana mai cewa, “harin na biyu an yi amfani da makami mai linzami mai na cruise.”
Kakakin ya kara da cewa, “Dukkan hare-haren biyu sun sami nasarar kai wa ga wuraren da aka nufa.”
Haka nan, kakakin ya bayyana cewa dakarun sojojin sama, na makamai masu linzami, da na ruwa na Yaman sun gudanar da wani farmakin hadin gwiwa kan jirgin yakin Amurka USS Harry S. Truman da wasu jiragen yaki da ke rakiyarsa a arewacin Bahar Maliya.
“Wannan farmakin ya yi amfani da jirage marasa matuka da makamai masu linzami, kuma shi ne hari na takwas da aka kai wa jirgin tun isowarsa tekun Bahar Maliya,” in ji Saree.
Harin ya cimma nasarorin da aka sanya a gaba, inda ya tilasta wa jirgin yakin Amurka barin wurin da ake gudanar da farmaki.
Gargadi mai tsauri ga Amurka da Isra’ila
“Rundunar Sojin Yaman tana gargadin dukkanin dakarun da ke gaba da mu a Bahar Maliya da su guji yin wani yunkurin kai hari kan kasarmu yayin tsagaita bude wuta a Gaza. Duk wani irin hari za mu mayar da martani da matakan soja masu tsanani da ba su da iyaka ko jan layi,” in ji Saree.
Jami’in ya bayyana cewa hare-haren an kai su ne domin nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinawa da ake zalunta da mayakansu, tare da mayar da martani kan kisan kiyashi da ake yi wa Falasdinawa a Gaza.
Ya kara da cewa, duk da amincewar majalisar ministocin gwamnatin Isra’ila kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, har yanzu suna ci gaba da aikata hare-hare masu tsanani.
Hare-haren, in ji Saree, wani bangare ne na mataki na biyar na goyon baya a yakin da aka sanya wa suna “Alkawarin Nasara da Jihadi mai Tsarki.”
Ya kuma jaddada kudurin dakarun na ci gaba da kai hare-hare muddin gwamnatin Isra’ila ta ci gaba da yaki da kuma kawanya mai tsanani da take yi wa yankunan Falasdinu.
Dakarun Yaman sun fara kai hare-harensu kan wuraren Isra’ila tun watan Oktoban 2023 domin tallafawa Gaza da Lebanon, wadanda suka fuskanci yakin kisan kare dangi da kuma karin hare-haren ta'addanci daga gwamnatin Isra’ila.
Hare-haren da dakarun Yaman suka kai, wadanda suka sami nasara, sun zo ne kafin da kuma bayan munanan hare-hare da gwamnatin Isra’ila, Amurka – babbar kawarta – da Birtaniya suka kai kan yankin Yaman.
Dakarun Yaman na mayar da martani ne ta hanyar kara kai hare-hare kan kadarorin Isra’ila da na Amurka, ciki har da jiragen yakin Amurka da jiragen ruwa masu dauke da jiragen yaki da aka jibge a gabar tekun Yaman.