Kasar Masar ta ce Isra'ila za ta saki fursunonin Falasdinawa fiye da 1,890 a madadin Isra'ilawa 33 da ta kama a zangon farko na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
A ranar Laraba, an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta matakai uku tsakanin Hamas da Isra'ila domin dakatar da yakin da haramtacciyar gwamnatin Isra'ila ke yi a Gaza.
Ma’aikatar harkokin wajen Masar a ranar Asabar tace, za a sako fursunonin a cikin kashi na farko na kwanaki 42 na tsagaita wutar, wanda zai fara aiki da karfe 8:30 na safe agogon kasar ranar Lahadi.
Tun da farko Isra'ila ta ce za a 'yantar da fursunonin Falasdinawa 737 — babu ko daya kafin karfe 14:00 agogon GMT, Lahadi.
Ana kuma sa ran za a sako mutanen kasashen waje, ciki har da Amurkawa, tare da Isra'ilawa guda 33 da aka kama, kamar yadda CNN ta ruwaito, inda ta nakalto daga majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin.
Daga cikin ‘yan Isra’ila 251 da Hamas ta yi garkuwa da su a lokacin Dufanul Aqsa a yankunan da aka mamaye a ranar 7 ga Oktoba, 2023, 94 har yanzu suna Gaza, ciki har da 34 da sojojin Isra’ila suka ce sun mutu.
A ƙarshen kashi na farko, fursunoni 65 za su kasance a Gaza. Za a yi shawarwarin sakin su — wasu daga cikinsu na iya kasancewa sun mutu — za a yi shawarwari daga ranar 16 ga yarjejeniyar.
Masar da Qatar su ne manyan masu shiga tsakani da suka taimaka wajen daukar tsawon lokaci ana kokarin kawo karshen kazamin yakin da Isra'ila ta yi na kisan kare dangi da kabilanci a zirin Gaza, wanda kuma ya shafe sama da watanni 15 a karkashin gwamnatinsu.
Yanzu Masar ta ce za ta kuma samar da "shigar da manyan motoci 600 a kowace rana zuwa Gaza, gami da tirelolin mai guda 50," a cewar ministan harkokin wajen kasar Badr Abdelatty.
Ya ce tirelolin mai guda 50 za su shiga yankin da aka yi wa kawanya da zarar an fara tsagaita wuta a ranar Lahadi.
"Muna fatan manyan motoci 300 za su tafi arewacin zirin Gaza."
Tsagaita wutar ta zama mahimmin lokaci don isar da agaji cikin yankin. Daruruwan manyan motoci ne tuni suka yi layi a mashigar kan iyakar Rafah, wadda aka rufe tun watan Mayu.
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce yarjejeniyar tsagaita wuta abu ne mai sauki, amma mafari ne na magance manyan bukatu na jin kai, na tunani, da na likitanci a Gaza.