Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Seyyid Ali Khamenei, ya bayyana jimamin sa game da shahadar wasu manyan alkalan Iran guda biyu a wani harin ta'addanci da aka kai a birnin Tehran.
Shahararrun alkalan — Ali Razini, shugaban reshe na 39 na Kotun Koli, da Mohammad Moqiseh, shugaban reshe na 53 — an kashe su ne a wani harin ta'addanci da aka kai a ginin Kotun Koli da ke tsakiyar birnin Tehran a ranar Asabar.
Alkalan sun yi aiki kan shari'o'in yaki da laifuffukan da suka shafi tsaron kasa, leken asiri, da ta'addanci.
A cikin wani sako da ya aike ranar Asabar, Jagoran Juyin Juya Hali ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan alkalan biyu bisa alhinin rasuwarsu.
Jagoran ya ce Razini ya kasance an yi yunkurin yi masa kisan gilla daga wasu makiyan sa a baya, kuma ya sha wahala a matsayin tsohon soja, yana mai cewa wasu daga cikin ‘yan uwansa biyu ma sun yi shahada.
Ayatullah Khamenei ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya ba da rahama da ta'aziyya ga iyalan su tare da ba su hakuri.
A cikin wani sako daga shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana ta'aziyyarsa game da shahadar Alkalan biyu a wani harin ta'addanci na "matsorata" da "rashin bil'adama". Ya jaddada cewa jami'an tsaro da hukumar tabbatar da doka su dauki matakin gaggawa wajen gano wadanda suka aikata wannan laifi.