Jiragen yaƙin Amurka sun kai hare-hare da dama a arewacin babban birnin Yemen, Sana’a, bayan da sojojin Yemen suka ɗauki alhakin kai farmaki kan jirgin ruwan USS Harry Truman a Tekun Bahar Maliya.
Tashar talabijin ta al-Masirah ta Yemen ta ruwaito cewa, an kai hare-hare guda huɗu a yankin al-Azraqeen da sanyin safiyar Lahadi.
Har yanzu ba a bayyana irin asarar rayuka ko dukiyoyi da aka yi sakamakon hare-haren ba.
Wannan farmaki ya zo ne awanni bayan kakakin sojojin Yemen, Birgediya Janar Yahya Saree, ya bayyana cewa sojojin ƙasar sun kai hari kan jirgin ruwan USS Harry Truman “ta amfani da jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami” a Tekun Bahar Maliya.
Ya kuma gargaɗi “mayaƙan gaba a Tekun Bahar Maliya kan sakamakon duk wani hari da za su kai wa [Yemen] yayin lokacin tsagaita wuta a Gaza.”
Wannan hari na baya-bayan nan ya zama na takwas da sojojin Yemen suka kai kan jirgin ruwan Amurka tun bayan shigarsa Tekun Bahar Maliya a watan Disamba.
A matsayin nuna goyon baya ga Falasɗinawa a Gaza, sojojin Yemen sun fara kai hare-hare kan kadarorin Isra’ila da na Yammacin duniya tun watan Nuwamba 2023, bayan Isra’ila ta fara yaƙin ta’addanci a Gaza a watan Oktoba 2023, tare da maida martani ga hare-haren Amurka da Birtaniya a ƙasar Yemen.
Don matsawa Isra’ila lamba ta kawo ƙarshen yaƙin ta’addanci a Gaza, sojojin Yemen sun fara kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke da alaƙa da Isra’ila, Amurka, da Birtaniya.
Sakamakon waɗannan hare-hare, tashar jirgin ruwa ta Eilat da ke kudu a yankunan da aka mamaye ta kasance a rufe gaba ɗaya, abin da ya jefa tattalin arzikin Isra’ila cikin ƙunci.
Sojojin Yemen sun sha alwashin ci gaba da kai hare-hare har sai Isra’ila ta dakatar da farmakin da take yi a ƙasa da sama a Gaza.
Tun bayan fara yaƙin, Isra’ila ta kashe aƙalla Falasɗinawa 46,899, yawancinsu mata da yara, tare da jikkata mutum 110,725 a Gaza. Har yanzu dubban mutane ba a gansu ba, ana zaton suna ƙarƙashin ɓaraguzain gine gine.