Tsagaita wuta a Gaza bai kamata ya ba da damar karin kwace yankuna a Yammacin Kogin Jordan ba: Kungiyar Kiristocin Falasɗinu

 


Kungiyar Kiristocin Falasɗinu tayi gargadi cewa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza bai kamata ta zama hanyar da za a ci gaba da kwace filayen Falasɗinu a Yammacin Kogin Jordan ba, ko kuma ta haifar da wani sabon yunƙurin kashe-kashe da korar Falasɗinawa daga gidajensu.

"Muna jaddada cewa abin da ke faruwa a Gaza bai kamata ya zama akan Falasɗinawa a Yammacin Kogin Jordan ba, ciki har da al-Quds. Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza bai kamata ta zama hanyar kwace ƙarin filayen Falasɗinu ko wani yunƙurin kashe-kashe, lalata gidaje da korar mutane, tare da amincewar wasu manyan ƙasashe na Yamma da ke ci gaba da manufofin mulkin mallaka a kanmu ba," in ji Kairos Palestine a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.

"Wannan wahalar da ake fama da ita a Gaza bai kamata ta zama hanyar rufe ido ga matsalolin Falasɗinawa a sauran sassan ƙasar ba, ciki har da yankunan da aka kwace tun daga 1948," in ji sanarwar.

Sanarwar ta miƙa gaisuwa ga jaruman Falasɗinawa da suka nuna ƙarfin hali a wannan lokaci mai wuya, tare da jimamin asarar rayuka fiye da 47,000 da dubbannin raunika.

Sanarwar ta kuma jaddada buƙatar yin adalci, bin doka ta duniya, da farfado da Gaza.

Kungiyar ta yi kira ga shugabannin Falasɗinawa da su haɗa kai da kawo ƙarshen mamayar Isra'ila.

"Ta hanyar haɗin kai za mu iya tabbatar da makoma mai kyau ga duk Falasɗinawa."

Post a Comment

Previous Post Next Post