Isra’ila ta janye shari’ar sojojin da ake tuhuma da kashe wani mayaƙin Palasɗinu

 


Isra'ila ta janye bincike akan sojoji biyar da ake tuhuma da kashe wani mayaƙin ƙungiyar Hamas ta Palasɗinu, wanda aka kama a farkon kwanakin yaƙin ƙisan kiyashi akan Gaza.

Babban Lauyan Ƙasa, Amit Isman, ya sanar a ranar Litinin cewa an rufe shari’ar da ake yi wa Roi Yifrach, Yisrael Biton, Sahar Ofir, Akiva Kaufman, da Israel Peretz, yana mai cewa babu laifin da aka samu.

Ya bayyana cewa ikirarin sojojin na kashe mayaƙin na Falasɗinu ƙarya ne kawai da nuna alfahari.

A wani bincike da aka yi a watan Nuwamba na 2023, Ofir ya ce Yifrach ya nuna masa bidiyon da ya nuna yana daba wa wani Bafalasdine dake ɗaure wuka a fuska har sai da ya mutu.

Duk Yifrach da Ofir sun amince a cikin saƙonnin WhatsApp cewa sun kashe mayaƙan Palasɗinu ba a lokacin faɗa ba, inda Ofir ya amince da aikata cin zarafin jima'i.

Isra’ila ta kaddamar da farmakin ta mai tsanani akan Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, bayan Hamas ta aiwatar da wani farmaki mai tarihi akan haramtacciyar Kasar don ramuwar gayya bisa zaluncin ta da ya ƙaru akan al’ummar Palasɗinu.

An tilastawa Isra’ila amincewa da tsagaita wuta bayan ta kasa cimma manufofinta duk da kashe sama da Falasɗinawa 47,000, mafi yawansu mata da yara, a Gaza.

Sojojin mamayar sun wallafa bidiyoyi a dandalin sada zumunta, suna nuna yadda suke aikata manyan laifukan yaƙi akan Falasɗinawan cikin farin ciki.

A watan Oktoba na 2024, cibiyar Hind Rajab Foundation (HRF) — kungiyar data samo suna daga yarinya ‘yar shekara shida ta Palasɗinu da aka kashe cikin rashin tausayi — ta shigar da ƙarar hukuma a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) akan sojojin Isra’ila 1,000 bisa manyan laifukan yaƙi da suka aikata a Gaza da ke karkashin mamaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post