Masu harbin bindiga na Nesa (Snipers) na Isra’ila sun kashe yara biyu ’yan Falasɗinu a Rafah duk da tsagaita wuta

 


Harbin bindiga daga Isra’ila ya kashe yara biyu ’yan Falasɗinu tare da jikkata wasu a birnin Rafah da ke Gaza, duk da tsagaita wuta da ke gudana tsakanin Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa, Hamas.

Zakaria Hamid Yahya Barbakh ya rasa ransa ranar Litinin kusa da Dandalin al-Awda a kudu da birnin Rafah, inda shaidu suka dauki bidiyon sojojin Isra’ila suna harbin wani mutum da ke kokarin daukar gawar yaron.

Rahotanni sun ce ku wani yaro dan Falasdinawa ya rasa ransa, yayin da wasu tara, cikinsu har da yara, suka jikkata a harbin bindigar Isra’ila a Rafah tun da farko a wannan rana.

Majiyoyin Falasdinawa sun bayyana cewa tankunan Isra’ila sun karya iyakokin da aka kayyade, inda suka yi luguden wuta kan fararen hula. Majiyoyin sun ce sojojin sun kutsa zuwa nisan mita 850 (kafa 2,789) cikin yankin, wanda ya zarce iyakar mita 700 da aka amince da ita a yarjejeniyar tsagaita wuta.

Yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce ta fara aiki ranar Lahadi, an tsara ta ta dawwama na tsawon kwanaki 42 tare da tanadin tattaunawa kan matakai na gaba, karkashin jagorancin Masar, Qatar, da Amurka. A matsayin wani bangare na yarjejeniyar, Hamas ta sako mata uku ’yan Isra’ila a musayar fursunoni 90 ’yan Falasdinawa, yawancinsu mata da yara.

Yayin da tsagaita wuta ke ci gaba a Gaza mai cike da rikici, tashin hankalin Isra’ila na kara kamari a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

’Yan kungiyar Yahudawa, tare da goyon bayan sojojin Isra’ila, sun yi barna a kauyukan Yammacin Kogin Jordan da ke arewacin al-Quds, inda suka kona gidajen Falasdinawa, wata makarantar yara, da wani kasuwanci na cikin gida.

Ofishin Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya (OHCHR) a Falasdinu ya bayyana damuwa kan “zubar jini na tashin hankali” da ’yan kungiyar Yahudawan da sojojin Isra’ila ke yi a Yammacin Kogin Jordan, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ke aiki a Gaza.

Baya ga tashin hankalin da ’yan kungiyar Yahudawan ke yi, sojojin Isra’ila sun kafa wuraren binciken soji tare da rufe hanyoyi a fadin Yammacin Kogin Jordan, inda suka hana ’yan Falasdinawa zirga-zirga.

Rahotannin kafafen yada labaran Falasdinawa sun ce duk wata hanya da ke kaiwa al-Khalil, Qalqilya, da Salfit, tare da wasu garuruwa da kauyuka a yankin Salfit, an rufe su, haka kuma matakai makamantan haka sun shafi Bethlehem.

A wani lamari mai nasaba da wannan, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wata doka da ta soke takunkumin da aka kakaba wa Yahudawan da ke zaune a Yammacin Kogin Jordan, wadanda gwamnatin Joe Biden ta aiwatar a baya a matsayin yunkuri na yakar abin da suka kira "motsin tsagerun mazauna."

Post a Comment

Previous Post Next Post