Babban jami’in sojin Iran ya bayyana cewa kasar za ta halarci atisayen sojojin ruwa na duniya da rundunar sojin ruwan Pakistan za ta shirya, wanda aka tsara za a fara a watan gobe.
Babban hafsan sojin kasar Iran, Manjo Janar Mohammad Baqeri, ya yi wannan furuci ranar Litinin game da atisayen AMAN (Zaman Lafiya)-25, wanda za a gudanar a birnin tashar jiragen ruwa na Karachi daga ranar 7 zuwa 11 ga Fabrairu.
“Iran ta sami gayyata don halartar wannan atisaye na kasa da kasa a Pakistan, kuma za mu halarci wannan taron,” in ji shi.
Wannan taron ya ja hankalin kasa da kasa sosai, musamman da ake sa ran Rundunar Sojin Ruwan Jamhuriyar Jama’ar Sin (PLA Navy) za ta taka muhimmiyar rawa a atisayen.
Baqeri ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Babban Hafsan Sojin Pakistan, Janar Asim Munir, a babban birnin Islamabad, inda Baqeri ya kai ziyara tare da tawagar manyan hafsoshin soja.
Jami'an sun jaddada cewa dole ne kasashen su yi yaki da ta'addanci da gaske domin tabbatar da tsaron dindindin a yankunan iyakar su.
Baqeri ya kuma bayyana cewa kasashen sun samu ci gaba mai kyau a tattaunawarsu ta bangarori biyu, musamman a fannin soji da kuma fannin kariya.
Ya kara da cewa an dauki “matakan asasi” don rufe iyakokin, domin zirga-zirgar tsakanin kasashen ta kasance ne kawai ta wuraren shige da fice na hukuma.
Jami’in ya yi nuni da karfin gwiwar Pakistan wajen yaki da kungiyar ta’addanci ta Jaish al-Zulm (Rundunar Zalunci) da ke da sansani a Pakistan, yana mai cewa hadin kai a yankunan iyaka da saurin musayar bayanan sirri za su taimaka wa kasashen wajen gudanar da gaggawar ayyukan yaki da ‘yan ta’adda.
Babban kwamandan sojin Iran, a lokaci guda, ya yi maraba da bude kasuwannin iyaka tsakanin Iran da Pakistan, wanda zai zama mataki na kawo karshen fasa-kwabrin kaya da kuma tallafa wa harkokin kasuwanci.