Sojojin Isra’ila sun harba harsasai da hayaki mai sa hawaye kan iyalan Falasɗinawa da ke jiran sakin fursunoni a wajen gidan yarin Ofer

 


Sojojin Isra’ila sun kai hari da harsasai da hayaki mai saka hawaye kan iyalan fursunonin Falasɗinawa da suka taru a wajen gidan yarin Ofer, da ke Yammacin Kogin Jordan, suna jiran sakin ‘yan uwansu a cikin yarjejeniyar tsagaita wuta.

An kai harin ne a wajen gidan yarin Ofer, a ranar da ake sa ran za a sako 90 daga cikin fursunonin a cikin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma da ƙungiyar Hamas.

Yarjejeniyar da aka fara ranar Lahadi, ana sa ran za ta kawo ƙarshen yaki mai tsawon wata 15 wanda Isra’ila ke yi a Gaza wanda ya zuwa yanzu ya kashe kusan Falasɗinawa 47,000, mafi yawan su mata da yara.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Isra’ila sun raunata akalla Falasɗinawa 7 a lokacin harin.

Wannan zagaye na musayar fursunonin gwamnatin Isra’ila da Falasɗinawa ya kasance tare da matakan tsaro masu tsauri da sojojin Isra’ila da ’yan sanda suka kafa, wanda aka ce yana nufin hana taruwar jama'a.

Kafin sakin fursunonin, sojojin Isra’ila sun kai farmaki kan gidajen wasu matan Falasɗinawa da ke cikin garin al-Quds mai tsarki da Isra’ila ta mamaye.

Sojojin mamaya sun kuma gargadi iyalan fursunonin kan kada su yi murna ko ɗaga tutocin Falasɗinu, tare da barazanar cewa hakan na iya haifar da a soke sakin.

Wannan ya biyo bayan maganganun Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, wanda ya ce Tel Aviv tana da "hakkin" ci gaba da yaki da Gaza duk lokacin da ta ga dama.

Netanyahu ya yi wannan furucin duk da amincewar gwamnatin da yarjejeniyar, da kuma gargadin ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinu kan sake kunna farmakin sojojin Isra’ila.

Post a Comment

Previous Post Next Post